MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZANUN part 10

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman

Part 10.
Malukussaifi ya ce,”To kai kuwa lluru ina kake nufin za ka kai
mu iluru ya amsa masa, “Ka sani fa yanzu ba kai kake iko da ni ba
domin ka yi sakaci ka rabuda allonka, saboda rashin sanin amfanina
Ka manta duk wahalar da ka sha ka samu allon nan, amma duk kamanta
ka rabu da wannan allo. To yanzu wanda ya mallaki wannen allon shi ya
umarce ni da na dauko ku na yadda ku.
Da Malukussaifi ya ji haka, sai ya tambayi lluru, “Shin yanzu
waye ya mallaki wannan allon kuma ya umarce ka da ka aikata mana
haka?” Ya amsa masa ya ce, “Waye kuwa in banda uwarka wadda ka
baiwa allon. Ita ce ta umarce ni da na aikata muku wannan, kuma ka
sani ba ni da ikon saba umarnin wanda duk ya mallaki wannan allo.
Saboda haka kada ka zarge ni sai dai ka zargi kanka da yin sakaci da
allonka da ka yi.” Da ya ji wannan bayani na Iluru, sai ya yi nadama
da rabuwa da allonsa ya kuma nemi iluru da ya ajiye su wuri daya tare
da Shamatu, amma ina, ya ce ai ba shi da ikon yin hakan.
Bayan wani dan lokaci sai su ka iso birmin Daudanu, nan sai Iluru
ya sauko kasa ya ajiye Shamatu ya kuma tashi da Malukussaifi ya nufi
birnin Gailanu da shi. Alokacin da ya sauke Shamatu, sai ta zauna
tana kukan bakin cikin rabuwa da mijinta da iyayenta. Haka ta kasance
cikin wannan hali har gari ya waye, da ta ga gari ya waye sai ta tashi
ta fara tafiya ba ta san inda za ta ba. Ta yi ta tafiya har rana ta
take, kafarta ta rika konewa da zafin rana ga kishirwa ga yunwa, sai
ta fara kuka tana cewa,”Ya Ubangiji kai ka shigar da ni wannan hali
saboda haka ka kubutar da nı daga wannan bala’i da na abka cikinsa.
Tana cikin wannan hali sai ta hango wasu dogwayen gutane manya
manya su arba’in bisa dawaki sun nufo ta, su kuwa mutanen wannan
birni na Daudanu ne. Yayin da suka karaso wurin Shamatu sai suka
tsaya suna kalonta, daya daga cikinsu sai ya ce da sauran,” Kun ga
wata ‘yar karamar halitta mai ban mamaki, ai sai mu dauke ta mu kai ma
Sarki ita.” Sai ya mika hanmu ya dauki Shamatu kamar wanda ya
dauki takalmi. Suka koma izuwa cikin birni suka kai ta wurin
Sarkinsu, wanda ake kira da suna Akilu, suka nuna masa ita
Ko da Sarki Akilu ya ga Shamatu, säi ya ce, Ya ya za ku kawo mini wannan, da ganinta laifi ta yi wa Ubangijinta ya mayar da ita
karama haka, sannan kuma ku kawo min ita, ai kawai ku je ku mayar da
ita inda kuka ganta ku yanka ta a can. Da Shamatu ta ji wannan
magana ta Sarki sai ta ce, Wallabi dama ai haka Ubangijina ya yi ni,
ba wani laifi na yi masa ba.
Ana cikin haka sai ‘yar Sarkin wadda ake kira Sadika, ta shigo
wajen, ko da ta ga Shamatu sai ta kura mata ido. Ta ga kyakkyawa ce
kwarai amma ga ta ‘yar karama, sai ta tambayi ubanta ta ce, Wannan
fa uban ya ba ta labarin yanda aka tsinci Shamatu kuma ya gaya
mata ya umarci mutanen da suka kawo ta da cewa su mayar da ita inda
suka dauko ta su yanka ta.
A nan sai Sadika ta ce, Ai ba haka bane, dama na taba samun
labari cewa akwai kananan mutane kamar ta, ba wani laifi ta yi ba
dama haka take, yanzu kawai ai sai mu kai ta wajen abin bautarmu
Idan ya karbe ta ya yarda da ita, to shike nan sai mu bar ta a wajensa
ta rika yi masa hidima, idan kuma bai karbe la ba, to shike nan sai
mu yanka ta.” Uban Sadika ya yarda da wannan shawara ta ‘yarsa, ya
kuma yi mata izini da ta kai Shamatu wurin wanan Gunki nasu.
Sadika ta kama hannun Shamatu suka nufi wajen da wannan abin
bautawa na su yake, da zuwansu sai Sadika ta bude kofar wani daki
Suka shiga. An bi bangon dakin an yi masa ado da dinare, ga shimfidu
na kilisai, daga can gefe an yi wasu kwami-kwami na azurfa guda
biyu, daya an cika shi da zuma daya kuma an cika shi da ruwan
matsatsen lemo da abarba da nikakkiyar ayaba da ruwan inibi. Daga
wani gefen kuma an ajiye wata tasa da kaji guda uku a ciki, daya
soyayyiya daya gasasshiya, daya kuma dafaffiya. A tsakiyar dakin ga
wani katon rago a kwance duk an yi wa kahonsa da kofatonsa ado da jan
dinare da lu’u-lu’u.
Da shigarsu dakin sai ragon nan ya yi ku ka. Sadika sai ta ce.
Ai shike nan kin yi sa’a, abin bautarmu ya karbe ki, yanzu ma barka
da zuwa yake yi miki” Shamatu ta tambaye ta, Ina Ubangijin naku
yake ne?
Sadika ta amsa mata la ce. ai wannan ragon da kike gani, shi
Ubangijin namu, shi muke bautawa. To yanzu abin da nake so dake
Shi ne, za ki zauna anan duk lokacin da ragon nan ya bukaci ya sha
ruwa ki dauki tasar nan ta dinare ki debo zumar can ki hada da wancan
ruwan ya’yan itatuwan nan ki ba shi ya sha. Haka kuma idanya bukaci
Cin abinci, ki dauki waccan tasar mai gaman kajin can a ciki ki ba
shi yaci, shi ne abincinsa, kullum za a rinka kawo miki gurasa guda
biyu ita ce abincinki. Sannan kuma ki kiyaye, kullum idan kika ga
ragon nan zai yi fitsari ko ya fara ki yi maza ki sa tasa ki tari
fitsarin domin kullum da shi Sarki yake wanke ido. Haka kuma duk sanda
ya yi kashi ki share ki kwashe ku zuba a wannan tasar domin muna
hadawa da shi wajen yin maganin cututtuka.” Bayan ta gama yi mata
wannan bayani, sai ta fita ta mai da kofa ta rufe ta bar Shamtu da
rago.
Ko da Shamatu ta ga Sadika ta tafi, sai ta ce, Mahaukatan
banza, wai ku rasa abin da za ku bautawa sai rago.” Shamatau ta ci
ta sha daga abincin nan na rago ta koshi, ta zauna har dare ya yita
tashi ta share dakin tas ta tara kashi da fitsarin rago kamar yadda
Sadika ta gaya mata.
Da gari ya waye Sadika ta zo ta ga dakin ragon nan ya yi fes an
share, ta ga ga fitsari da kashin ragon nan Shamatu ta tara, sai ta
ji dadi ta ce, “Madalla dake wannan bakuwa, haka nake so ki kyautata
ga wannan abin bauta namu, me yiwuwa ma shi kansa ya ji dadi ya
taimakeki ki ya mayar da ke wurin yan uwanki. ta karbi wannan najasa
ta kawo kaji guda uku da zuma da ruwan matsattsun ‘ya’yan itatuwa ta
ce. Ga abincinsa.” Sannan ta miko gurasa guda biyo ta ce, ga
naki abincin.”
haka kullum ake yi, kullum idan an kawo abincin nan sai Shamatu
ta baiwa ragon nan gurasar nan ya ci ita kuma ta cinye wadannan Kaji ta sha zuma ta sha wadannan ‘ya’yan itatuwa. Idan kuma ragon ya yi fitsari ko kashi a kan shimfidar kilisan nan sai ta dauki tsumangiya
ta zane shi har sai da ya zamto ragon nan ba ya fitsari ko kashi sai
in ita ta tara sannan ya yi, ta tarbiyantar da ragon nan da
haka ta kasance cikin wannan hali.
Shi kuma can Malukussaifi lokacin da Iluru ya ajiye shi a bimin
Gailanu sai ya rinka tafiya ya ga dogayen bishiyu ga wata korama ruwa
na gudana, gefen ta ga ya’yan itatuwan nan iri daban-daban ya ci ya
koshi ya kuma sha ruwan koramar nan sannan ya cigaba da tafiya har
yamma ta yi sai ya zo gindin wata doguwar bishiya sai ya kamata ya
hau can samanta ya zauna yana hangen kasa
Zamansa ke da wuya sai ya hango wani fatalwa tsoho yana tahowa
inda yake. Ko da ya zo kusa sai ya ga fatalwar kansa kato kuma
lailayayye kamar bal, ga manyan idanuwa da nanannen hanci ga jikinsa
duk gashi kamar dabba. Yana zuwa daf da wanan bishiya sai ya jiyo
kanshin Malukussaifi ya daga kansa sama ya hango shi ya tsaya ya kura
masa ido kur yana kallon sa har tsawon kimanin sa’a guda, sannan sai
ya juya ya komà ta hanyar da ya biyo.
Da Malukussaifi ya ga fatalwar nan ya juya ya tafi sai ya yi
ajiyar zuciya ya godewa Allah. Jum kadan sai ya hango wannan
tsohon ya komo tare da wadansu falalwoyin ‘yan uwansa ya kirawo su
Suka karaso suka taru suna tallonsa can sai suka juya gabaki daya
suka koma ta hanyar da suka biyo. Ganin haka sai abin ya ba wa
Malukussaifi mamaki ya zauna yana ta tunanin wanan lamarin, yana
cikin haka can sai ya kuma hango su sun dawo tare da wata tsohuwa mai
farin gashi kamar na rago da suka karaso wajen sa suka dube shi
sukai magana da wani yare wanda shi baiji abin da suka ce ba, sukai ta
magana da wanan yare can sai ya ga duk sun tafi sun bar tsohuwar nan
a wurin ita kadai.
Bayan tafiyar su sai tsohuwar ta yi masa nuni da hannu da ya
sako sai ya ce, Aa ba zan sakko wajenki ba domin kuwa in na sakko
cinye ni za ki yi.” haka tai tai da shi ya sakko ya ki, sai ta vi
masa magana da yarensa ta ce, Ka gasgata ni ka sakko zan taimake ka
na kubutar da kai daga wadanan fatalwi yan’uwana ba za su yi maka
komai ba don inda ina so su cinye Ka da tuni na sa sun jefo ka sun
cinye ka, kuma ka ga idan na barka a nan har dare ya yi to za su zo su
cinye ka a nan, saboda haka ka gasgata ni ka sakko.”
Da ya ji haka sai ya mika lamannsa wurin Ubangiji sai ya sakko

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*