MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZANUN book 2 part 9

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman
Part 9.
Ko da haduwar su sai aka kaure da yaki, a kai ta gabzawa,
Malukissaifi duk inda ya sa gaba sai ka ga gawawwakin mutane na zuba,
ya daga takobinsa ya yi kururuwa yana yi wa kansa kirari yana cewa,
“Ni ne Malukussaifi dan Sarki Ziyyazanun, dan Tabi’il Yamani, dan
Usudul bai’da, dan Samu dan Nuhu (AS)
Ko da Kamriyya ta ji haka sai ta san lallai Malukussaifi ne
danta, bai mutu ba. Sai ta ce a zuciyarta,
“Wato wannan tsinannen
dan nawa da na je na sassara bai mutu ba, ga shi har ya warke ya zo
yana yakina.” Sai ranta ya baci, ta yi wa mutanen ta tsawa ta ce,
Kai ku tsaya, ku daina yaki, wannan ai Sarkinku ne kuke yakarsa,
dana ne.” Yayin da jama’a suka ji haka sai duk aka daina yaki aka
tsaya.
Kamriyya ta sauko daga bayan dokinta: ta zo ta sumbaci kafar
malukussaifi tana kuka tana gaya wa mutanen ta. tana cewa, Ai wannan
shi ne Sarkinku. dan Sarkinku ziyazzanun. Saboda haka yanzu shi za
ku bi, dama ni wakiliya ce Kawai. Sanan kuma ta juya wajen
malukussaifi ta ci gaba da cewa, Ya dana abun da na aikata maka na
aikata maka ne a lokocin na rasa hankalina kamar yadda na gaya maka
a baya cewa wani lokacin na kan zama mara hankali wani lokacin kuma
mahaukaciya.
Tana fadar wadannan maganganu tana kuka, tana birgima a kasa tana
buga kanta a kasa tana cewa, Ya dana, kashe ni ka dau fansar abin
da nai maka, dama babu wanda ya dace ya kashe ni a duniyar nan in
ba kai ba, kashe ni na huta dana.
Shi kuma Malukussaifi da ya ga haka, sai jikinsa ya yi sanyi.
tausayinta ya kama shi, ya dauka da gaske take. bai san makirci ta ke
shirin kulla masa ba. Sai ya sauko daga dokinsa ya rungume ta yana
cewa, Ba komai, ai wannan abu Allalh ne va kaddara haka za ta faru
Tun da ga shi a dalilin hakan har ma na samo wasu muhimman abubuwa
ya nuna mata allonsa ya gaya mata amfanin sa ya kuma nuna mata
takobinsa ya ce, “Wadannan duk a gidan Kakana Samu na samosu
Saboda haka ki kwantar da hankalinki, wannan habu komai ya wuce
Kana ya nuna mata Shamatu, ya kwashe labarin ta ya gaya mata
Kamriyya ta rugume shamatu tana mai murna da matar danta. Sai
ta ce da Malukussaifi, Ai mu je ka shiga birninka ka hau karagar
mulkin ka, shike nan na huta
Suka dunguma cikin birni, Malukussaifi ya hau karagar mulki, a
nan ya yi godiya ga Allah, Sa’adunizzanji na zaune a gefensa. Haka
dai kullum Malukussaifi ya fito fada a yi fadanci ya koma har kwana uku. A rana ta ukun da safe kafin ya fito fada sai ya ga ran Shamatu
ya baci, hankalinta ya tashi. Sai ya tambaye ta ko me yake damun ta.
Shamatu ta ce, Ni yanzu kawai ina tunanin mahaifina ne, saboda
na san sakamakon wannan abu da ya faru babban Sarki Saifur’adu zai
dora masa laifi ne, saboda haka ina tsoron sharrin da zai kulla
masa.
Malukussaifi ya ce da ita, “Ba komai, yanzu zan sa lluru ya kawo
miki shi nan ki ganshi, kuma zan sa ya rika tsare masa garinsa.” Nan
da nan ya umarci lluru ya je ya dauko Sarki Afarahu.
Can kuma babban Sarki Saifu’ar’adu, ya kirawo bokayen nan nasa
guda biyu, Sakaradisa da Sakaradiyyuna, ya ce da su,Kun ga wannan
tsinannen ya dau ke Shamatu ya gudu da ita, wato ya haramta mini
auren ta kenan.” Sai bokayen suka ce, Ai wannan duk makircin Sarki
Afarahu ne, domin kuwa ba yadda ba mu yi da shi ba, a kan ya kashe shi
tun yana yaro, amma ya ki, ya raine shi har ya girma, yanzu ga abin da
ya jawo mana nan.
Sarki ya ce, Lallai kuwa wannan magana taku haka take. Lallai
ku wa sai na hukunta Sarki Afarahu.” Sarki ya tura cikin yaudara a
ka kirawo Sarki Afarahu, ya ce yana so su yi wani sirri ne ya taho shi
kadai
Da zuwan Sarki Afarahu, sai Sarki Saifu’ar’adu ya sa aka kama shi
aka daure shi. Ya umarci hauni da ya sare masa kai, nan da nan hauni
ya zare takobi ya yi wo kansa. Ko da Sarki Afarahu ya ga hauni ya nufo
shi sai ya rintse idanunsa ya ce, ldan abin bautawar nan na su
Malukussaifi, wanda yake gAya mana gaskiya ne, to Ka kubutar da ni
Allah.” Rufe bakinsa ke da wuya. kafin hauni ya tarar da shi, sai Iluru ya zo ya dauke shi.
Sarki Afarahu na bude idonsa sai ya ga Malukussaifi da Shamatu
a zaune gabansa. Sai ya ce, “Mafarki nake ne ko gaske ne abin da
nake gani.” Malukussaifi ya ce, Ya kai azzalumin Sarki, ya za ka
zalunce ni ka aurar da yarka Shamatu ga wani bayan ka nemi sadakinta
na kawo? Wallahi ba don raino na da kai ba tun ina karami, da na kashe
ka.”
Sarki Afarahu ya ce, “Ya dana, wadannan abubuwa duk da ka ga sun
faru duk sharrin bokayen nan ne da sukai kulle-kullensu; ni kuma
saboda gudun kada babban Sarki ya cutar da jama’ata, tilas sai na bi
yadda suke so. Amma ni babu komai tsakanina da kai sai allheri. Ai da ni da shamatu tda mulkina duk naka ne, ai kawai bari gobe a daura
mumu aure a cigaba da biki.”
Da Malukussaifi ya ji wannan magana ta Sarki Afarahu, sai ya ce,
To babu komai na yafe maka” Ya kuma kirawo uwarsa Kamriyya su ka
gaisa da Sarki Afurahu, aka shiga maganar daurin aure.
Gari na wayewa Kamriyya ta bude taska ta debo wasu riguna irin
na mata wadanda aka saka su da farin alharini, a kai musu cín baki da
dinare ta bai wa Shamatu ta ce ta sanya, ta kuma debo sarkokin wuya
guda shida da abin kunne da abin hannu na dinare ta ba ta, da kuma
wasu takalma wadanda aka yi su da fatar zaki akai musu ado da gashin
jimina da dinaare duk ta hada ta ba ta ta sa.
Can shi ma malulaussaifi ya caba ado aka fito wajen daurin aure,
inda a nan Kamriyya ya ta kawo wasu lailayayyun dinarai guda uku
wadanda kowannensu darajarsa ta kai kimar harajin kasar na shekara
biyar, ta bayar da su ta ce gasadakın bangarenta ran. Haka dai aka
daura aure a kai ta shagali har kwana bakwai.
A rana ta bakwai, wadda ita ce ranár da Malukussaifi zai shiga
dakin amaryarsa Shamatu, bayan da dare ya yi sai ya shigo wajen
mahaifiyarsa don ya yi mata sallama, ya kuma shaida mata cewar zai
shiga inda matarsa take. Sai Kamriyya ta ce To dana yau fa ita ce
ranar da za ka shiga wajen amaryarka, don haka ina yi maku addu’ar
Zahlu ta albarkance ku da iyali. To amma fa ka kiyaye da wannan allo naka, domin ka san mai tsarki ne kuma rike shi sai mai sarki.”
Malukussaifi ya yi mumushi ya shiga dakin da Shamatu take, ita
kuma Kamriyya ta koma ta zauna tana ta tunanin yadda za ta yi ta raba
shi da wannan allo nasa.
Jim kadan bayan rabuwarsu da danta, sai Kamriyya ta bi shi dakin
da yake, ta same shi tare da Shamatu suna hira irin ta mata da miji.
Da shigarta sai ta ce, Ya dana, ni dai iná dada gaya maka ka kiyaye
da wannan allon domin kada najasa ta same ka yana jikinka.”
Malukussaifi sai ya ce da ita, I, ai zan kiyaye Unmma, amma dai bari
in ba ki shi ki ajiye mini.” Ya dauka kaunarsa take. Kamriyya ta
karbi allo daga hannunsa ta fice tana murna da farin ciki.
Kamriyya ta dabi allon nan ta yi dariya ta ce, “Wai shi yanzu ya
dauka fa duk kaunarsa nake yi, wai shi ga mai uwa, ya dauki allonsa
ya ba ni To ni kuwa na rantse da zahlu, sai na halaka shi da wannan
allon nasa.
Yayin da Kamriyya ta koma dakinta sai ta goga wannan allo, nan
da nan sai lluru ya zo gabanta ya tsaya, ya ce, “Gani ya shugabata,
me kike so na aikata miki.” Kamriyya ta dube shi ta ce, Kai ne
iluru?” ya amsa mata ya ce NI ne ya shugabata.” Sai ta tambaye
shi, “Wadanne birane ne suka fi nisa da abin tsoro daga wannan birni
namu?”
lluru ya amsa mata, ya yi ta lissafa mata birane daban-daban, har
ya zo kan birnin Gailanu da birnin Daudanu. Sai ta tsai da shi a nan,
ta tambaye shi-ta ce, Shi wannan birnin Gailanu a ina yake, kuma
mene ne hadarinsa?” Ya ce, “Shi birnin Gailanu yana can gabas da
wannan kasa, kuma Fatalwoyi ne masu cin mutane a wannan birni.” Sai
ta sake tambayar sa ta ce, To shi kuma birnin Daudanu fa?
Ya kuma amsa mata ya ce, “Shi kuma wannan birni yana can ku
dancin Kasar nan, kuma mutanensa halittarsu sun fi ku girma da tsayi
kwarai da gaske.” Da ta ji wannan bayani na lluru, sai ta ce da shi,
To yanzu ina so ka dauki Malukussaifi tare da matarsa Shamatu, shi
ka jefa shi birnin Gailanu, ita kuma ka jefa ta birnin Daudanu. ka
dawo nan ka same ni.” Ko da lluru ya ji haka sai ya ce, Ya
shugabata, wannan fa danki ne na cikinki wannan kuma matarsa ce, don
haka ita ma yarki ce. Wane laifi sukai miki da za ki sa ni na aikata
musu haka? Kamriyya ta daka masa tsawa ta ce, Ni dai na ba ka
umarni kawai ka je ka aikata.
ai ko cikin wannan dane lluru ya shiga dakin da Malulkussaifi da
Shamatu su ke. ya tarad da su suna kwance suna barci ya dauke su ya
tashi sama da su ya kama hanyar sa ta zuwa bimin Daudanu. Yana cikin
tafiya, saboda iska sai su ka farka daga barcinsu gabadaya
suna
mamaki da tunanin cewa wai shin a ina ma suke ne. Can Malukussaifi ya waratsake daga magagin barcinsa ya gane a
wa ya dauko su sai ya tambaye shi.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*