MALIKUSSAIFI IBNI ZIYAZZANUN book 2 part 5 and 6

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman
Part 5.
.
Daya da ga tsuntsayen sai ya dubi dayan ya ce, “Shaihu Jayyada,
ka ga fa wannan uwarsa ce fa mahaifiya ta aikata masa wannan aiki,
Saboda kwadayin mulki kawai ” Sai daya tsuntsun ya amsa ya ce,
Haka ne Shaihu Abdussalam, amma ka ga da zai ci ganyen wannan
bishiyar ya shafa a jikinsa da sai ya warke sarai, kamar ma bai yi
Wani ciwo ba.”

Bayan sun gama zantukansu sai tsuntsayen suka tashi Suka tafi
Shi kuma Malukussaifi yana daga kwance ya ji duk maganganun
tsuntsayen nan sai ya kuma yin addu’a ya roki Ubangiji ya Kawo sababin yadda zai iya samun ganyen wannan bishiyar.

Nan da nan sai iska ta taso ta girgiza bishiyar ganyenta ya zubo masa a jiki, ya
Samu ya kama guda daya da lebensa ya auna ya hadiye, da yin haka sai
ya fara jin karfin jikinsa. ya mika hannu ya sake dauko ganyen ya rinka gogawa a jikinsa. Nan da nan duk jikinsa ya warke, ya mike ras,
kai ba ka ce ma wani abu ya taba Samunsa ba.

Ya tashi ya yi godiya ga
Madaukakin Sarki, ya hangi dokinsa yana kiwo. ya bi shi ya kama ya
hau ya kama hanya ya fara tafiya, ba tare da ya san inda ya nufa ba.

idan ya ji yunwa sai ya ci daga ya yan itatuwa. yana shan ruwa daga
kwazazzabai
Bayan Malukussaifi ya samu kwana arba in yana tafiya cikin daji.

Sai ya hango wasu manyan duwatsu guda biyu masu tsayi, tsakanin
duwatsun akwai kogi mai gudu ya raba su. Daya dutsen wanda daga
bangaren hagu wato bangaren da Malukussaifi yake ja ne, dayan kuma
na dama da shi fari ne.

Da ya karaso gindin wannan jan dutsen Sai ya ga wani kogo a
jikinsa, ya ji ana magana daga cikin kogon ana cewa, Barka da zuwa
Malukussaifi dan Sarki Ziyyazanun, dan Tabi’ul Yamani, dan Usudul
baida’a, dan Samu dan Nuhu Alaihissalatu wassalam. Sai ya ga wani
farin mutum dogo ya fito daga wannan kogon yana yi masa barka da zuwa
cike da farin ciki
Sai ya tambayi mutumin ya ce, Kai kuwa ya ya a kai har ka san
Sunana, bayan kuma kai ba ka taba gani na ba sai yau?” Sai mutumin ya ce, Ai yau shekara ta ashirin ina zaune a nan ina jiran zuwanka, domin na nusassheka aijiyar da kakanka SAMU ya yi maka, kuma ni ma dai na gaji wannan gadin a wajen babana, shi ma wajen kakana ya gada, Shi kuma a wajen nasa uban, shi kuma a wurin kakansa.

mutumin nan ya kama hannun Malukussaifi suka shiga cikin kogon
nan. da Shigar su sai wannan mutum ya yi tafi sai ga kujeru guda oiyu
an kawo tare da abinci. Suka zauna sai mutumin ya ce da Malukussaifi
ya ci wannan abinci. Shi kuwa sai ya ce, Ya ya za’ai in ci abincin alhalin ban ga wanda ya kawo shi ba, ai ba zai yiwu ba. Shin wai kai yaya
Sunanka ne kuma mene ne addininka?

Mutumin nan ya amsa masa da
cewa, ni sunana Ihimimiddalibi, kuma ni Malami ne. ina bin Addinin
Annabi Ibrahim (AS). Saboda haka ka gasgata ni ba zan cuce ka Da.

Da ya ji wannan bayani na Malam Ihimimuddalib, sai ya saki jikinsa
Suka kama cin abinci
Bayan Sun ganma cin abincin nan. sai Ihimimuddalib ya ce da Malukussaifi. To gobe da asuba za mu fita mu hau sanman dutsen nan zan jarraba ka domin na tabbatar da cewa kai ne mai wannan ajiya ko
kuwa ba kai bane.”

Nan suka kama zikirillahi har dare ya yi asuba ta
kawo kai, a wannan lokaci suka fito daga wannan kogo suka kama hawa
saman wannan dutsen. Da suka hau sai Malukussaifi ya ga wani al’amudi
dogo a tsakiyar dutsen a Jikin al’amudin ya ga wata matattakala da
sarkoki na kamawa a jikinta hagu da dama.

Sai ihimimuddalib ya
tambaye shi ya ce, Me ka gani? Malukussaifi ya ba shi
labarin abin da ya gani, a nan Malam Ihimimuddalib ya ce, Lallai
na yarda kai ne mai wannan ajiya ba shakka To yanzu mu sauka kasa mu
koma sai gobe da asuba mu komo nan zan nuna maka wannan ajiya taka.”

Suka sakko suka komo cikin wannan kogo suka cigaba da zikirullahi
Asuba na yi suka kuma hawa sáman wannan dutsen, Malam lhimimu ya
tambayi Maukussaifi ya ce, “Me ka gani? Ya amsa masa ya ce, Na
kuma ganin abin da na gani jiya. ihimuddalibi ya kuma cewa da shi,To wannan matattakalar da ka gani jeka ka taka ka hau ta zuwa
kan wannan al’amudin.” Malukussaif ya tattaka ya hau kan al’amudin
ya tsaya.

Sai Malamin ya ce, to hanga kan daya dutsen, wancan farin ka ga me ka hango?” Sai ya hanga ya ce, “Na hango takun sawaye guda biyu a kan dutsen. Kuma na hangi wani farin gida kato mu mai katuwar kofa

ihimimuddalibi ya ce, “Lallai na kara yadda cewa kai
ne mai wannan ajiyar, domin in ban da haka, babu mai iya ganin
wadannan abubuwa. To yanzu ka sa Allah a zuciyarka, ka yunkura da nufin tsallakawa kan wancan dutsen, kawai za ka ga ka haye sawayenka Sun dira cikin takun sawayen nan da ka hango.”

Malukussaifi ya ga nisan da ke tsakanin dutsen da yake kai da
kuma dayan, ya kuma kalli kasa ya ga kogin nan da ke tsakani, sai ya
ce,Haba Malam, ya za ai na yi tsalle na dira a can, ai in nai tsalle ruwan nan zan fada na mutu kawai, Ni ba zan yi ba naki.” Sukai ta.
jayayya da kyar Malam Ihimimu ya shawo kan sa ya yarda zai tsallaka.

Nan dai Maiukussifi ya dangana, ya yunkura kamar yadda Malamin
ya umarce shi, sai kawai ya ga ya dira a kan daya dutsen to a wannan
lokacin shi kuma lhimimu ya yi kiran wasu sunayen Allah sai shi ma ya
tsallaka ya dire a kusa da shi.

A nan shi ya ce da Malukussaifi, to ka tafi izuwa kofar wannan gidan ka tsaya ka fadi nasabar ka (sunan iyaye da kakanni), za
ka ga kofar ta bude, sai ka shiga. ldan ka shiga za ka ga gawar wani
mutum dogo a kwance a kan wana katon gado na farin karfe, fuskarsa a
lullube da mayafai guda takwas Sannan za kä ga ya dora hannunsä na
dama ya dafe kirjinsa, hannunsa na hagu kuma ya mike shi bisa gadon
idan ka je sai ka tsaya a a gefen hannunsa na dama ka fadi nasabarka,
ka ce ga ka ka zo karbar ajiyarka, to sai ka daga hannunsa na dama
wanda ya dafe kirjinsa. Za ka ga wani dan allo na bakin karfe
da sarka a jikinsa ka dauko allon ka fito ka dawo nan”
Malukussaifi ya nufi kofar gidan nan, da zuwansa daf da kofar sai
ya ce, “Ni ne Malukussaifi dan Sarki Ziyyazanun, dan Tabi’ul Yamani
dan usulul baida’a, dan Samu dan Nuhu Alaihissalam.

Yana gamawa sai kofar ta bude ya shiga ya aikata kamar yadda Malam Ihimimuddalib ya
umarce shi da aikatawa. Ya dauko wannan allo ya fito ya dawo wurin
Malamin.
Malam ihimu ya kalli allon yace Ka kawo na rike maka, ka kun komawa cikin gidan amma yanzu idan ka je ka tsaya a hannunsa na hagu
Ka kuma fadar nasabarka ka zura hannunka karkashin shimfidar da yake
kwance za ka ji wani takobi, to ka dauko shi ka rataya shi a wuyanka.

Ka yi masa sallama ka fito ka komo nan.” Ya kuma gargade shi da kada
ya kuskura ya ce zai bude fuskar wannan gawar ta kwance.

Malukussaifi ya kuma komawa cikin wannan gida ya yi kamar yadda
aka umarce shi, ya dauka takobin ya rataya shi a wuya, ya yi sallama ya juyo, zai fito. Kafin ya fito sai ya yi tunani, wata zuciyar ta
raya masa cewa, ai kawai ya koma ya cire mayafi na farko ya cire na
biyu har zuwa na karshe, sai ya ga kowaye a kwance. Jarumin sai ya
koma cikin gida ya aikata abin da zuciyarsa ta shirya masa.

Sai ya ga mutum fari mai yanayin kamanni inin nasa. Yana cikin wannan hali sai
ya ji ana girgiza gidan kamar zai rushe, ya ji an buge shi ya fadi
sumamme, aka watso shi waje aka mai da kofa aka rufe
Can bayan ya farfado daga sumansa, sai ya ga ihimimi na tsaye a
kansa.

Malam ya ce, “Kai dai wannan da taurin kai kake, wane kai da
bude fuskar yayan Annabawa. Ai wannan da ka bude fiskarsa Samu ne
dan Annabi Nuhu (AS), in banda kai jininsa ne da yau kwananka ya
kare, don ni ma da ina da ikon kashe ka da kashe ka zan yi bisa ga
wannan laifi da ka aikata. To amma yanzu hukuncin da zan yi ma shi
ne, ba zan haura da kai can ba a nan zan barka, sai an jima” Malam
Ihimimu ya yi addu’a ya yunkura ya tsallako ya bar Malukussaifa
wannan waje.

Malukussaifi ya nemi lhimimu ya rasa, ya yi, ya yi, ya tsallaka
ya kasa, sai ya hakura ya kwanta ya kama barci.Can bayan ya farka
sai ya ga tasa da zuma a ciki da gurasa, ya duba bai ga wanda ya kawo
ba, abinka da mai jin yunwa, sai kawai ya dauko gurasar nan da zuma
ya rinka tsoma yana ci har ya koshi.

Yana gama wa sai ya ga an ajiye
masa ruwa a wata tasa amma bai ga wanda ya kawo ba, ya dauka ya sha
haka dai akai ta yi har kwana arba’in.
Wata rana sai ya rinka tunanin cewa to shi a nan zai mutu kenan,
kullum ai ta kawo masa abinci iri daya, wannan ba za ta sabu ba.

Makukussaifi ya yanke shawara a kan ya rungumi kaddara kawai ya fada Cikin kogin nan idan ma mutuwa ce ya mutu ya huta kawai yana gama yanke Shawararsa sai kawai ya yi tsalle ya fada cikin kogin nan S3canin wadannan duwatsu. Nan fa ruwa yai ta hautsina shi ya yi kokarin ya yi iyo amma ina ba dama.

ruwan nan haka yayi ta hautsinawa da shi, ya sha ruwa ya cika masa ciki. Da ya ga ya tasamma halaka sai ya yi wata addu’a ya ce, “Ya Ubangiji, ldan ajalina ne a
wannan ruwan to Karaba ni da wannan wahalar na mutu na huta.

idan kuma ba a nan ajalina yake ba to Ka kubutar da ni daga wannan wahalar da
nake ciki.”
Rufe bakinsa ke da wuya sai wani katon dutse ya gangaro ya fado
cikin ruwan tinjim, ruwan ya yi tsiri sama ya komo yif ya rufe shi,

sai ya sume. Ruwan ya ci gaba da tafiya da shi har zuwa inda yake
fadawa cikin wani babban kogi, ya fado da shi cikin wannan babban
kogi inda nan kuma igiyar ruwa ta kora shi gefen kogin.

Ruwa dai yana
tafiya da shi har zuwa wani waje inda rassan wata katuwar bishiya
suka shigo cikin ruwan, yana zuwa nan sai wani reshe ya rike kubakar
wandonsa ya tsaya a nan.

Jim kadan ya farko daga sumansa ya ga a halin da yake, sai ya
kukuta ya kama reshen nan ya yunkura ya haye can saman bishiyar nan
ya rabu da ruwa.

Bayan ya dan huta ya komo cikin hayyacinsa, sai ya
hango ganuwar wani dan karamin birni, koda ya ga haka sai ya yi
hamdala ya godewa Ubangji wanda Ya sa ya hangi gari, zai je ya tarar
da mutane yan’uwansa.

Sai ya diro kasa daga kan wannan bishiya daga shi sai bante ga
takobinsa na rataye a wuyansa, ya kama hanyar shiga wannan birni wanda
ya hango. Yana cikin tafiya har ya isa bakin kofar birni, sai ya ji ana cewa yauwa ga bakonmu nan ya zo, maza ku kamo shi mu
kashe shi” Koda Malukussaifi ya ji haka, sai ya juya a guje ya koma
ya hau kan wata bishiya ya buya.

Yana daga nan ya hango wasu mutane
kimanin su dari uku sun nufo gindin ishiyar nan da yake kai.
Da zuwansu sai babban Su ya kafa kujerarsa a gindin wannan
itaciya ya ce da sauran ku bazu ku nemo mana wannan bako namu.

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman
Part 6.

Duk suka bazu suna nema har rana ta yi zafi suka komo Su ka ce ba su
ganshi ba. Shi babban nasu sai ya ce. To mu ci abinci ku koma don
kuwa ba zamu koma gida ba sai da wannan bako.

Suka kawo abinci su ka
zauna suna ci, shi kuma can Malukussaif kanshi yana bugarsa, abinka
da mai jin yunwa, amma duk da haka ya hakura bai motsa ba.
Haka dai sukai ta yi har kwana biyu, a rana ta biyun da su ka
fara cin abinci sai Malukussaifi ya raya a zuciyarsa ya ce, ai
fa na ki sauka daga bishiyar nan yunwa ma sai ta halaka ni.

Gara ma
na sauka mutanen nan su kashe ni na huta, ko ba komai dai na roke su
su ba ni abinci na ci -kafin su halaka ni, balle ma in har suka ba ni
abinci na ci, don su dari ukun nan cikin kankanin lokaci duk zan gama
da su.” Kawai sai ya sauko cikin mutanen nan.
Ko da suka gan shi sai sukai caraf suka kama shi suna,cewa, Ga
bakon nan ma, ga bakon nan ma.”

Shi kuwa sai ya ce, Ku tsayya, ni
ba rigima za mu yi da ku ba, ni yanz ku bani abinci na ci tukuna,
bayan na ci sai ku aikata abin da kuke so game dani.” Sai babbansu
ya ce, Ai ba wani Bata lokaci mu kai shi wurin shugabanmu” Su ka
tafi da Malukussaifi cikin wannan birini, da zuwansu sai Suka kai shi
gaban wani saurayi wanda ya nada farin rawani kuma ya ja amawali ya
rufe fuskarsa, sai idonsa kawai
ake iya gani.

Mutanen nan suka gaida wannan saurayi, ya dubi Malukussaifi ya
ce, Kai ya sunanka, kuma mutimin wace kasa ne kai kuma me ya kawo
ka wannan gari namu?”

Malukussaif ya yi mamaki yayin da ya ji
muryar saurayin nan ta mata ce. Sai ya ce, Ni yanzu ba wani bayani
da zan iya yi maka har sai ka ba ni abinci na ci tukuna ko me ma kake
so ka tambaye ni sai ka tambaye ni, domin ni yanzu yunwa nake ji.
Nan da nan saurayin nan ya sa aka kawo masa abubuwan ci da na
sha, aka ajiye a gabansa.

Malukussaifi ya dira a kan abinci, yi yalke
yana korawa da abubuwan shan da aka kawo masa har ya fara kaiwa
mashafar turare. Da ya fara koshi sai kuma ya shiga ci a hankali, duk
laumar da ya dauko sai ya ce, Bari in yi launmar karshe a
rayuwata.” Haka dai ya yi ta yi har ya gamna cin abincin nan Da ya kanmmala abin da yake sai saurayin nan yä ce da mutanensa Ku riko shi mu kai shi wurin babana” Suka tafi da Malukussaifi Zuwa wani babban gida dake tsakiyar birnin.

suka shiga da shi cikin
wannan gida suka kai shi gaban wani dattijo. Wannan saurayi ya ce da
shi Mun zo da shi” da dattion nan ya dago fuskarsa sai
Malukussaifi ya ga ashe Malam Ihimimuddalib ne, ya ce, Barka da
zuwa Mlalukussaifi dama ina nan ina jiran ka; ka zo in ba ka allonka

Malukussaifi ya dube shi ya ce,Haba Malam ya ya kai da ka gudu ka barni a can kan dutsen gidan Samu na mutu. yanzu kuma ka ce kana jirana wannan ma ai zancen banza ne. lhimimi ya ce, Kayi ya shugabana, ai a wannan lokacin ni ba ni da ikon da zan
tsalloko da kai, saboda bude faskar Samu daká yi. Shine wannan wahalar ta
sauka a kanka a matsayin fansar abin da ka aikata, amma ni Allah Ya
sanar da nj akwai sanadin da zai kawo ka nan, in ka lura lokacin da
kake kan dutsen nan kullum ba kaganin gurasa da zuma ba to ai ni nake
kai ma Ai ni mai kaunarka ne ya shugabana.

Malukussafi ya gasgata wannan magana ta malam lhimimu, ya ku
ma tambaye sho ya ce, ina allon nawa Kuma ina so ka gaya mini amfanin wannan allo.

Malan Ihimimi amsa ya ce,Shi dai
wannan allo asalin sa na kakanka Samu ne shi Kuma wanan allo akwai
wani aljani mal suna iluru wanda ya ke masa hidama.

Duk wanda ya
mallaki allon nan aljani iluru ya zama bawansa, duk lokacin da va
goga allon da hannu sau uku, iluru zai zo ya biya masa dukkin irin
bukatunsa to ka ji wannan shi ne amfanin allon nan Yanzu allon yana hannun yata Jizatu, saboda na gani cikin alkaluma cewa ita ma tana daga Cikin matayen da za ka aura
shi ya sa na ba ta la rike maka kafin zuwanka.

” ko da Malukussai ya ji
Wannan magana ta Malam ihimimudalib sai ya ce to yanzu ina yar taka take lhimimu ya ce, Ga ta nan kusa da kai, ai wannan
saurayin da kake gani ba namiji bane ita ce
Jizatu, ta kwance rawanin dake kanta ta yaye fuskarta ta dubi
Malukussaifi shi ma ya dube ta: ya ga kyakkyawace kwarai da gaske.

tana da manyan idanuwa da kyawun sura da dirin jiki irin wanda maza suke sha’awa, nan suka ci gaba da hira har la’asar ta yi. Suna cikin hira can ihimimuddalib ya dubi Malukussaifi ya ce,Ya shugabana to yanzu bukatarka ta biya, ka zo na baka ajiyar da
kakanka Samu ya ajiye dominka. Yanzu ni kuma ina so ka biya min tawa
Bukatar kamar yadda na biya maka taka,

Malukussaifi ya ji wannan magana ta Malam Ihimimu sai ya tambayeshi Wace bukata ke gareka a wajena? Malamin ya amasa masa
da cewa, bukata ta ita ce ka auri wannan ‘ya tawa jizatu, kamar
yadda na gaya maka na gani a cikin alkaluma tana daga cikin matayeka
da za ka aura, to wannan kawai ni shi ne bukatata.”

Yayin da Malukussaifi ya ji wannan magana ta Malam ihimimu, sai
yace, ai shi sam wannan magana ba za ta yiwu ba, domin kuwa ya yi
alkawari a ba zai auri wata mace ba, sai ya fara auran Shamatu ya
Sarki Afarahu. Haka dai sukai ta jayayya tsakanin sa da Malam ihimimu amma , ya tsaya kai da fata a kan ra’ayinsa.

Aokacin da suke wannan jayayya ita kuwa Jizatu tana wani daki kusa da su tana jin su. Ko da ta ji Malukussaifi ya ce ba zai aureta
ba Sai ya auri wata, sai kishi ya kamata ranta ya baci kwarai tai bakin ciki. A sakamakon haka sai ta yanke shawarar cewa tun da wannan
allo yana wurinta, in dare ya yi za ta goga shi aljanin nan Iluru ya
zo ta sa shi ya dauki Malukussaifi ya kai shi can wani wurin da ba zai
ta fa komawa cikin mutane ba, ya ajiye shi ya kare iyakar rayuwarsa acan.

Jizatu tana cikin wannan tunanin sai Ihimimu ya shiga dakin da ta ke ya iske ta a zaune ta yi shiru. Da shigarsa sai ya ce, Ya
yata me Kike tunani a kai ne, na ga kin yi shiru ke kadai?” Jizatu
ta gaya masa ai ta ji iokacin da suke jayayya da Malukussaifi yana
cewa ba zai aure ta ba. Sai ya auri wata shi ne abin ya bata mata rai hatma ta gaya masa shawarar abin mda ta yanke a zuciyarta za ta aikata
gare shi sakamakon kin auren ta da ya yi.

da malam ihimimu ya ji haka sai ya ce,”Ai dama shi wannan lamari rubutaccen al’amari ne daga Allah gara ma ki hakura ki ba shi allonsa, domin ba za ki taba yin nasara a kansa ba.”

Bayan da dare ya raba, sai Malukussaifi ya tashi ya yi addu’a ya
roki Allah ya taimake shi ya je ya dauko allonsa daga wajen jizatu
Ya nufi dakinta yana kiran sunayen Allah yana tafiya cikin sanda har
ya kai ga kofar dakin. Ya sa hannu ya bude kofar dakin a hankall ya
shiga ya tarar da ita ta yi nisa cikin barci, ya kuma ga allon
daure a dantsen hannunta na dama.

Ya lallaba ya kwance allon daga
jikinta a hankali ba tare da Jizatu ta farka ba, ya fito ya koma
dakinsa ya zauna ya yi wa Allah godiya.
Bayan da gari ya waye rana ta dan daga, Malukussaifi ya fita ya
je wurin Ihimimi ya tarar da shi suna zaune tare da yarsa Jizatu ya
shiga ya zauna suka gaisa ya ce Toni da ma na zo yi muku sallama
ne, domin yanzu zan Koma wurin mutanena da na baro su a can bayan
birnin Yemen. Saboda haka ina yi muku godiya bisa ga duk irin
taimakon da kukai min” Ko da Jizatu ta ji haka sai ta ce,To
tunda tafiya zakai baka biya bukatar babana ba, bazan baka allonka
ba.” Ta shafa ba ta ga allon ba, sai ya yi dariya ya ye ce, kin ga
allona nan” Ya gogi allon, nan da nan sai ga aljani iluru ya zo, ya
umarce shi da ya dauke shi ya kai shi birnin Yemen inda ya baro
mutanensa.

Ya yi masu sallama iluru ya dauke shi suka tafi
Can kuma Sarauniya Kamriyya bayan ta bar Malukussaifi cikin jini
lokacin da ta sassare shi da ta taho ba ta zame ko ina ba sai garim
babban Sarki Saifu’ar’adu, da zuwanta ta.nufi fada akai mata iso
wajen Sarki.

Sarki ya ce a shigo da ita, da zuwanta ta fadi gabar sa ta yi gaisuwa.
Sarki ya dube ta ya ce, Munafuka, wato mun tura ki ki kashe
sarkin Yemen, Sarki Ziyyazanun tun shekaru ashirin da daya da suka
wuce shi ne baki aikata hakan ba, har ma kika zamo matarsa har kike
girman kai garemu, wai kina jin ke ma shugaba ce, ba kya biyan mu
haraji Shi ne yanzu kin ga mun tura miki rundunar mayaka za su
fatattaka birninki, kika zo.”

Kamriyya ta ce, Zahlu ta baka yawan rai, wace ceni Ka tuna fa
ni kuyangarka ce, ka tura ni don na kashe Sarki Ziyazanun, a lokacin da na je na rasa hanyar da zan bi na aiwatar da sakon ka har sai da
na saki jiki a wurin Sarkin ya dauke ni mata a wajensa, sannan na samu
damar aiwatar da sakon ka na káshe shi. To a lokacin da na kashe shi
na samu ciki da shi, kima kafin ya mutu ya yi wa mutanensa wasiyyada
Su bi ni a matsayin Sarauniya, har sai dan da na haifa ya girma
na sauka na mika masa mulki.

haka kuwa ya kasance, bayan ya mutu mutanensa suka nadani sarauniya bisa ga biyayya ga umarnin Sarkinsu Ni kuma don kar na ki su nada wani ya zo yana gaba da kai, sai na yarda na karba. Bayan wani
dan lokaci sai na haifi da namiji, da ya kwana bakwai sai na daukeshi na kai shi daji na yar da shi don kar ya girma ya hau mulki addu’ar nan ta annabi Nuhu (A.S) ta tabbata a zamaninka shine wani tsinannen Sarki a karkashin mulkinka ya tsinceshi ya raineshibhar ya girma shine ka tura su yanzu su yakeni.

kuma na gane lallai dana ne dana yar. nan da nan na dsuko mutanen ubansa suka tabbatar masa lallai ni uwarsa ce ya yarda, ya kuma gaya min cewa sunansa Malukusaifi dan sarki ziyazzanun ko wa ya gaya masa ubansa oho.

to a wannan lokacin ne na hilace shi na ja shi daji na ce zan nuna masa dukiyar ubansa, bayan mun yi ta tafiya ya kwanta yana barci ni kuma na sassarashi na kashe shi, saboda cika umarninka da tabbatar da mulkinka yanzu shaura dayan makiyinka wanda ka tura su yake ni waishi sa’adunizanji, ai kai baka sani ba shi ma wannan makiyin ka ne shi zai taimakawa wannan dan nawa wajen hambare maka mulkin ka.

Ni yanzu abin da nake so ka rubuta takarda zuwa ga babban
sadaukinka, wanda ka tura su tare, ka umarce shi da ya yi biyayy gareni shi da sauraun mutanensa, su taimaka mu kama shi wannan
Sa’adunizzanjin, mu kawo maka shi gabanka ka aikata masa duk hukuncin da ka so Ni kuma na dawo nan gurinka na ci gaba da yi maka hidima tun da na kawo karshen wannan tsinannen.”

Da sarki ya ji wannan magana tata, sai ya ji duk irin abubuwan da Ta yi har ga shi ta kashe danta na cikinta sai ya gasgata lamarinta

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*