MALIKUSSAIFI book 2 part 1 to 4

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman

Part 1.

A littafi na farko idan mai karatu bai manta ba, mun tsaya a
inda Aljana Akisa ta dawo da Malukussaifi birnin Kaimaru daf da
rijiyar nan da Sarki Kamrunu ya sa aka jefa shi, ta yi masa
sallama ta tafi bayan ta ba shi hular sa wadda ya samo.

Malukussaifi ya tsaya yana tunanin yadda zai yi ya shiga
birnin Kaimaru saboda yana tunanin ko ya sanya hularsa ta bata
ko dakon garin nan wanda ake kira gammazi zai ganshi saboda na tsafi ne, haka dai ya tsaya yana ta tunani a bakin kofar shiga birnin Kaimaru.

Can kuma a cikin birnin Kaimaru Damatu yar bokanya
Akila tun ranar da Sarki ya sa aka jefa Malukussaifi a rijiya duk
ta rude, hankalinta ya tashi domin ta san ba makawa sai va
halaka,sai ta samu uwarta bokanya Akila ta ce da ita, “Ya ke
wannan uwa tawa ma’abociyar yawan hikimomi, da kin buga
kasa kin bani labarin Malukussaifi tun kafin zuwansa kuma har
kika gaya mini ai shi ne ma mijin da zan aura to amma ga shi
yau sarki zai halaka shi, saboda haka yanzu ya zama dole a kan
ki ki yi amfani da
irin hikimominki na tsafi ki kubutar da shi in kuwa ba haka to
lallai ni ma zan kashe kaina na huta da radadin begensa da yake
damuna.”
Ko da uwar ta ji haka ita ma sai hankalinta ya tashi jin
yarta ta ce za ta kashe kanta sai ta ce, Ki yi hakuri, ki kwantar
da hankalinki, zan yi iyaka bakin kokarina sai na ga na kubutar da
shi da ga wannan halaka da ya abka.” Haka tai ta yi mata dabara
Tana rarrashinta har zuwa wannan rana da Aljana Akisa ta dawo
da Malukussaifi bayan wannan garin
Awannan ranar bokanya Akila tana gida tana buga kasa tana
bokancinta, a cikin haka sai ta hango Malukussaifi a bayan gari
yana tunanin yadda zai yi ya shigo ba tare da Gammazi ya yi
masa komai ba. Ko da ta ga haka sai ta yi kiran yarta Damatu
ta gaya mata, Ai ga Malukussaifi can a bayan gari yana tunanin
yadda zai yi ya shigo. yanzu sai ki yi maza ki je ki same shi ki ce da shi ya shigo duk ta inda yake so domin kuwa gunkin nan
gammazi tuni na lalata shi. Suna cikin haka sai suka ji ana
bubbuga kofar gida, bokanya ta ce. To shi ke nan ma ya hutar
da mu, ga shi can ya shigo yana buga
kofa maza je ki. ki bude masa ya shigo,” Damatu ta yi zumbur
ta mike ta nufi kofar gida ta zare sakata ta bude kofa. Ko da su
kai ido hudu da Malukussaifi sai suka rungume Juna suna
shisshidar numfahi irin na ma’abota bege, sannan suka shiga cikin gida wurin uwarta, ita ma ta yi masa
maraba a kai masa shimfida ya zauna sannan suma suka zauna
tare da shi. Zaman su ke da wuya bokanya Akila ta mika hannunta baya
ta jawo wani katon tire wanda yake cike da abinci da na sha iri-
iri, suka ci suka sha, amma Damatu ta kasa cin abincin saboda
bege tana zaune kurum ta kurawa Malukussaifi ido tana kallonsa
tana mai cike da buri da bege
Bayan da ya huta ya kwashe labarın duk abin da ya faru tun
da ga lokacin da aka jefa shi a rijiya har zuwa wannan rana da
Aljana Akisa ta dawo da shi ya gayawa bokanya da yarta kuma
ya nuna musu hular da ya samo. Bayan haka ya kara da cewa,
To ni fa ba zama ne ya kawo ni ba. yanzu ina dabarar yadda
zan yi na dakko littafin nan na Halwanu
Bokanya ta amsa masa da cewa. to ai yanzu wannan abu
mai sauki’ne tun.da ga wannan hula taka, ai za ta taimaka maka
kwarai Yanzu yau shauran kwana biyar ranar zuwa bautar
wannan littafi ta zo sai ka bari a wannan ranar zan fita tare da
kai ka saka hulanka yadda babu wanda zai ganka idan mun je
mun yi sujjada Sai kawai ka dauko ka fito.” Ya yi na’am da
wanan shawara ta ta suka ci gaba da zama har kwana biyar wato anar fita bautar ta zo.
A Wannan ranar bokanya ta yi shiri ta fita izuwa fada sauran
bokaye. na biye da ita, cikinsu hadda Malukussaifi, amma babu
wanda yake ganinsa saboda ya saka hularsa. Da zuwansu fada Suka tarar wuri ya cika macik da jama’a,bokanya akila da Jama’arta suka nemi wuri suka zauna shi kuwa Malukussaifi ya je
gaban Sarki ya zauna babu wanda ya ganshi jim kadan Sarki yà yi umarni a tashi a tafi wajen bauta,
Sarki da bokanya da duk sauran jama’ar gari aka tashi aka
Qunguma zuwa wajen bautar littafi. Da zuwansu Sarki da kansa
ya sa makulli ya bude kofa suka shiga da duk sauran jamaa,
Sannan ya kuma dakko wasu ‘ya’yan makullan ya bude adaka ta
farko ya bude ta biyu ya bude ta uku ya ga littafi yana nan
yadda yake, nan ya sunkuya yana mai wa littafi sujjada.
Ko da Malukussaii ya ga haka duk sun sunkuya sai ya nufo
wannan littafin kafin ya kai ga inda littafin yake sai littafin ya
fado gabansa, ko da Sarki da sauran jama’ar dake kusa suka ji
motsin fadowar wannan littafi, duk sai suka mike suka ga littafi
na gewayawa amma ba su ga kowa a wurin ba. Sai suka tsaya
Suna kallo , shi kuma Malukussaifi da ya ga haka sai ya sa hannu
ya dau littafin yana dauka sai
jama a suka daina ganin littain.
koda ganin haka Sarki Kamrunu ya yi wa mutanensa tsawa ya
umarce su da su fita duk inda wannan littafi ya shiga su nemo
masa shi. Ran Sarki ya baci hankalinsa ya tashi idanuwansa suka
kada sukai jazur kamar an hura wuta. Haka jama’a sukai ta jewa
har dare’ ba su ga iittafi ba, a karshe dai suka zo suka gaya wa
Sarki cewa sun gaza samo wannan littafi.
Sarki ya juya ya dubi bokanya Akila ya ce,Ya ke
ma’abociyar yawan hikimomi da dabaru na mika wannan lamari
a hannunki, ki san duk yadda za ki yi ki ga kin gano inda
wannan littafi ya shige.” Da akila ta ji wannan magana ta Sarki sai ta
ce ai wannan abu ne mai sauki, da sannu zan binciko maka
inda wannan littati yake, kai sai ma na kawo maka wanda ya
dauke shi nan gabanka.” Haka dai ta yi tai wa Sarki kalamai na
na
lami, da kartafa gwuiwa har iyarsa ta yi sanyi sannan ya sallami
jama’a kowa ya tafi zuwa gidansa.
bokanya Akila na komnawa gida Sai ta tarar da Malukussaifi yana zaune ga hula ga littafi a gabansa, ta nemi wuri ta zauna.
Zamanta ke da wuya sai ya ce,To ni fa yau bukata ta ta biya
tun da na samu littafin nan gobe zan kama hanyar komawa garin
mu, kuma ina matukar godiya ga dukkan irin taimakon da ki kai
min ba zan taba manta wa dake ba.”
Da ta ji haka sai ta ce, “I, ai kuwa lallai bukatarka ta biya,
amma kuma ni ma ina so ka cika mini burina kamar yadda naka
ya cika. Burina kuwa shi ne ka auri ‘ya ta Damatu ma’abociyar
kyawu kafin ka bar garin nan. Wannan kawai shi ne bukata ta.”
Ko da ya ji wannan magana sai ya ce shi sam wannan ba za ta
yiwu ba, domin ya riga ya yi alkawarin ba zai auri wata ya mace
ba har sai ya auri Shamatu ‘yar Sarki Afarahu, haka sukai ta
jayayya da shi da ita, amma sam ya ki yarda.
Can ita kuma Damatu tana daga dakinta, tana jin duk irin
jayayyar da suke yi, ko da ta ji ya ce ba zai aure ba ta, sai ranta
ya baci hankalinta ya tashi, haka ta raba dare tana tunani, can sai
ta tashi ta shiga dakin da Malukussaifi yake kwance, sai ta tarar
da shi ya yi nisa a cikin barcinsa, sai ta dauke hular nan tasa ta
yi kokarin ta dauke littafin ammna sai tai gudun kar ya farka
saboda da shi ya tada kai sai ta hakura ta koma dakinta da
hular.
Gari na wayewa Malukussaifi ya farka daga baricinsa ya
duba ya ga bai ga hularsa ba, nan da nan ya tambayi bokanya ko
ita ta dauka, ta ce ba ta dauka ba. Suna cikin haka sai Damatu
ta shigo ta ce masa, “Ni ce na dauke hular kuma ba zan baka ita
ba, har sai ka aure ni.” Da jin wannan sai ya yi shiru, can sai ya
tuna da hudubar da Shaihu Jayyada ya yi masa ta cewar ya
dogara ga Allah, a dukkan lamarinsa.
Nan da nan sai ya fusata ya ce, Ba zan aure ki ba, hula
kuma ki rike, ni na dogara da Allah shi zai kubutar da ni.” Ya
tashi ya yi musu sallama ya kama hanyar sa ta komawa gabar
kogin nan da dabbar nan Hashisha ta kawo shi.
Ita kuma bokanya Akila bayan da rana ta dan daga, sai ta yi Shiri ta tafi fada. Da zuwanta ta fadi gaban sarki ta yi gaisuwa ta
nemi wuri ta zauna, zamanta ke da wuya,sai Sarki ya dube ta ya
Ce Ya ke mai yawan hikimomi ya labarin littafi me kika gani
game da shi kuma?”
Akila ta ce, Ai wato wanda ya dauki wannan littafi ai
yanzu ma ga shi can ina kallonsa ya kama hanyar zuwa bakin
kogi, yanzu maza ka sa a bi shi a kamo shi.”
Nan da nan Sarki ya yi tsawa, sadaukai mayaka duk suka
mike ya umarce su da cewa maza su bi wannan mutumin su
kamoshi. Nan da nan suka daurawa dawaki sirada suka hau, kimanin mutum dari biyar suka bazama neman Malukussaifi.
Shi kuma can Malukussaifi ya samu kwana biyu yana tafiya
cikin dajin yana Cin ya’yan itatuwa, yana shan ruwan
kwazazzabai. A rana ta uku, yana cikin tafiya sai ya ji karar
kofaton dawaki suna biye da- shi. Ko da ya waiga ya hango
mutanen nan da Sarki ya turo a sukwane kan dawaki, sai ya ranta
a na kare, ya yi ta gudu suna biye da shi har dare ya yi. Sai ya
Zo wani waje mai duwatsu cikin duhun dare, ya kwana karkashin
wani dutse duhu ya boye shi Su kuma mutanen nan su kai ta
neman sa amma ba su gan shi ba, sai suka tsaya suka tattare
hanyoyi suna jira gari ya waye Su kama shi
Da Malukussaifi ya ga haka sai ya yi tunanin a kan cewa
yanzu dabbar nan Hashisha tana kwance a gabar kogi, tana jira
rana ta bullo. A nan sai ya yi ta rokon Allah yana fatan ya boye
shi, ya wuce ba tare da mutanen nan sun ganshi ba. Allah ma ji
rokon bawañsa, ya amsa addu arsa. Haka ya fito ya ratsa ta cikin
mutanen nan ya wuce amma ba su gan shi ba.
Da zuwan Malukussaifi gabar kogi ya tarar da dabbar nan
Hashisha tana kwance. ya yi tsalle ya dafe gashin ta ya yi lif
Can su kuma mutanen dake neman sa, da gari ya waye ‘suka
duba ba su ganshi ba, sai suka rika bin sawunsa cikin yashi har
kusa da gabar kogi. A wannan lokacin ita kuma wannan dabbar ta fara ruri ta mike, mutanen nan duk Suka juya a firgice saboda jin
kukan Hashisha, suna cewa, Aiya, wannan ai ya hadu da
Hashisha ta lashe, ai sai mu koma mu ga ya wa Sarki.

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman

Part 2.

Haka suka
Koma gaban sarki a sukwane suKa shaida masa ai wanda ya dau
littafin Hahisha ta lashe shi.
Bayan faduwar rana Hahisha ta kwanta a waccan gabar
Malukussaifi ya sauka ya kama hanyar komawa hasumiyar
Shaihu Jayyada.

Da zuwansa ya yi masa sallama, Shaihun ya
amsa ya yi marhabin da zuwan Malukussaifi kuma ya kwashe
labarin duk abin da ya faru gareshi a tafiyarsa ya gaya masa,
kamar yana nan akai ya gaya wa Malukussaifi.

Sannan kuma ya
tuna masa da cewa shi gobe zai mutu, idan ya mutu, ya yi masa
wanka ya sa likkafani ya rufe shi, sannan kuma zai ga wasu
mutane sun zo jana’ izar sa ka da ya yi wa kowa magana daga
cikinsu.

Haka kuma bayan an gama zai ga sun koma, kada ya
waiwaya har sai ya daina jin motsinsu, sannan ya binne Shi ya
yi tafiyarsa.

Asuba na yi Shaihu Jayyada ya cika, Malukussaifi ya aikata
komai kamar yadda ya umarce shi. Bayan ya gama tsaf. ya kamo
dokinsa ya yi masa sirdi ya hau ya kamo hanyar komowa kasar
Duwar.

kasar Sarki Afrahu inda aka raine shi.
Can kuma a kasar Duwar din Sa’adunizzanji ya kosa da rashin
dawowar Malukussaifi ubangijinsa. Wata rana Sarki Afarahu
yana fadarsa tare da sauran jama’a, ga boka Sakaradiyyuna na
zaune a gefen sa sai Sa’adunizzanji ya shigo fadar cikin fushi nan
da nan Sarki da sauran jama’a duk suka mike tsaye cikin rawar
jiki.

Sa’adunizzanji ya numfasa ya ce da Sarki, Wato kun tura
uban dakina neman wani littati kun tura shi ga halaka ko, to nan
da yan kwanaki kadan idan bai dawo ba na rantse da tauraruwa
zahallu duk garin nan sai na halaka ku.” Ya juya ya fice a fusace.

Ko da ya fita sai Sarki Afarahu cikin dimuwa ya dubi
Sakaradiyyuna ya ce, Ka gani duk kai ka jawo mana wannan bala’in. Boka Sakaradiyuna ya ce da Sarki Afarahu, Kwantar da
hankalinka, wannan ni zan sabbaba abin da zai halaka shi.”

Nan sai boka Sakaradiyyuna ya rubuta takarda zuwa ga dan uwansa boka Sakaradisa dake can fadar babban Sarki
Saifu’aradu. Ya kwashe labarin duk irin abubuwan da suka faru
game da lamarin Malukussaifi har zuwa inda ya nemi auren
Shamatu da yanda ya tura shi ya zo da kan Sa’aduninzanji, ya
kuma gaya masa yanzu ma ya tura shi ya nemo littafin Halwanu.

Sannan kuma ya ce da shi ya gayawa babban Sarki
Saifu’radu wannan labari, ya kuma gaya masa idan har wannan
yaro ya auri Shamatu to zai zamto sanadiyyar rushewar mulkinsa
sannan kuma zai mai da su bayi, addu’ar nan da Annnabi Nuhu
(AS) ya yi ta tabbata a zamaninsu.

Ya kuma ce ya gaya wa Sarki ya aiko wa da Sarki Afarahu
da kyauta ya kuma nemi auren Shamatu domin ya kare mulkinsa
daga kubucewa daga hannunsa. Ya kuma ce ka ga ko da wannan
yaron ya dawo mana a kan bukatarsa, sai mu ce ya taho wajen
babban Sarki ya karbeta, ballantana ma na san yanzu wannan
yaron ya halaka tuni.

da ya gama rubuta takarda sai ya bai wa wasu bayi su bakwai
ya ce su tafi can kasar babban Sarki Saifu’aradu su kai wa dan uwansa boka Sakaradisä wannan takarda nan da nan bayin nan
suka kama hanya kwanci tashi, har suka isa wanan kasa.

Da
zuwansu suka kai wa boka Sakaradisa wannan takarda, ya karba
ya bude.ya karanta ta sai ya mayar ya ajiye yana jiran gari ya
waye da safe ya tafi da ita fada ya karantawa Sarki Saifuar’adu
ita.

Waye war gari ke da wuya, boka Sakaradisa ya shirya ya tafi
fada, ya kwashe laberin dake cikin takardar nan kaf ya gaya wa
Sarki, kuma ya kwadaitar da shi auren Shanmatu. Ya umarce shi
da ya nemi aurenta kamar yadda aka rubuta a cikin takardar nan
Ko da Sarki ya ji haka nan da nan, sai ya sa aka kawo wasu
manyan adaku çike da dinari guda hudu, ya kuma sa aka kawo wesu adakun guda biyar cike da kayan ado irin na mata da abubuwa iri-iri na daga nau’in dukiya, sannan ya sa aka kirawo
wanj babban Sadauki daga cikin mayakansa, wanda ake kira manadihu, tsawonsa Kamu saba’in ne ga shi da manyan idanuwa jajaye, ga shi baki mai katon kai da gajeren wuya mai ladi da lafta-laftan kafafuwa.

Kai saboda gimansa ma
ba ya hawa doki sai giwa. Da zuwan Manadihu ya fadi gaban
Sarki yai gaisuwa. Sarki ya umarce shi da ya dauki wannan
dukiya ya tafi garin Sarki Afarahu ya kai masa ya kuma gaya
masa yana neman auren yarsa ne Shamatu.

ldan ya yarda ya
shaida masa ya dauke masa haraji na shekara bakwai kuma duk
sauran kasashen dake kusa da kasarsa, harajinsu na wadannan
shekarun ya karfa ya bashi. idan kuma ya ce ya ki to ka yake shi
da shi da Sa’adunizzanji, ka zo min nan da su a daure cikin
sarka,

Manadihu ya ce, An gama”
Nan da nan Manadihu ya koma gida ya yi shiri ya kuma zabi
sadaukai dubu wadanda zai tafi da su. suka kama hanyar zawa
garin Sarki Afarahu. Sukai ta tafiya dare da rana ba ji ba gani,
har suka iso kasar sarki Afarahu da zuwansu sarki ya tarye su
aka kai su masauki akai tai musu hidima har dare ya yi, sai Sarki
ya ce su huta sai gobe da safe ya ji abin da yake tafe da su.

Bayan da gari ya waye rana ta dan daga fada ta cika makil,
Manadkhu da sauran abokan tafiyarsa suka shigo fada domin su
isar da sakon bebban Sarki Saifura’adu a wajen Sarki Afarahu
bayan duk sun yi gaisuwa sun zauna, sai Sa’adunizzanji ya shigo
fadar.

Da shigowar sa sai aka mike tsaye har da Sarki Afarahu, sai Manadihu ne kawai bai mike ba yana zaune sai Sa’adunizzanji ya dubi Sarki ya ce, Wannan shi kuma waye shi
daga. ina ya zo wannan gari’ Sarki ya amsa masa ya ce, “Ai Wannan dan
aike ne daga babban Sarki Saifuar’adu.” Sa’adunizzanji ya ce,
To shi ya fika daraja ne da har kai za ka mike yana zaune?

Ya dubi Manadihu cikin fushi ya daka masa tsawa mai firgitarwa ya ce kai munafiki bakin kare me ya kawo ka nan? Manadihu ya fusata ya ce, yau ga la’anan ne, kai waye kai za kai min
wannan tambayar? Ko kai ne Sa’adunizzanji, wanda Sarki ya ce in kai masa kai a daure cikin sarka. To yau kashinka ya bushe,
abin da ya kawo ni wannan gari kuma shi ne babban Sarki ya turo ni na nema masa auren Shamatu ne idan kuma kun ki na yake ku.

Ko da Sa’adunizzanji ya ji wannan magana sai ya ce, Au matar ma uban dakin nawa ka zo nema to karya kuke.” Ya yi
wuf ya zare takobi kafin Manadihu ya ankara ya tsinke masa ka ya kashe shi.”

Da boka Sakaradiyyuna ya ga haka sai ya dubi Sarki ya ce,
La,la,la, to maza ka umarci duk jama’ar nan su yaki Sa’adunizzanji. In kuma ba haka ba, to wallahi Zan aikawa da babban Sarki in ce kai ne ka sa aka kashe dan aikensa Manadihu.”

Nan da nan Sarki ya umarci jama’arsa da sauran
sadaukan nan dubu su yaki Sa’adunizzanji da yaransa su tamanin
din nan. Nan da nan guri ya kaure da yaki aka yamutse ba ka iya
jn komai sai kuwwar mazaje da karar karafkiyar takubba da karar duka da kulki, haka a kai ta gwabza yaki har tsawon kwana uku.

A rana ta ukun ana cikin gwabza yaki Sa’adunizzanji ya gaji sun rufar masa gabadaya suna neman kama shi. Can sai suka hango wani sadauki a sukwane bisa doki.

Da zuwansa sai suka
gane ai Wahashilfala ne ya dawo. Ya kutso cikinsu yana kakkare
sara da bugu, can sai ya ga ai Sa adunizzanjl ne ake yaka. Koda shi Sa’adunizzanji ya hango shi sai ya ce da shi,Taimake ni,
saboda kai suke yakata.

Nan da nan Malukussaifi ya hau su da
sara da bugu da kulki da suka da mashi, cikin wasu yan sa’o’i ya yi musu muguwar barna ya rarake su, suka juya zuwa
gurin da Sarki yake zaune suka shaida maasa ai Wahashil fala ne fa ya dawo yake yakar su saboda haka Sarki ya tsayar da yaki in ba haka ba to zai karar da su a wannan rana.

ko da Sarki ya ji wannan labari sai ya mike ya hau dokinsa ya nufo filin daha ya yi tsawa da a daina yaki,

duk aka tsaya
cirko-cirka. malukussaifi ya yi wa kansa kirari ya yi kira ya kare da cewa ni ne Malukussaifi dan Sarki ziyyazanun
Sarki A farahu bu ya bugi dokinsa ya kusanci Malussaifi, da
Zuwansa sai ya sau ka daga dokinsa ya je gabansa ya durkusa yana
mai ladabi da kalamai na nuna nadama da neman gafara.

Ko da Malukussaifi ya ga haka, nan da nan shi ma sai ya sauko daga
dokinsa ya kama hannun Sarki ya ce, “ai kai ubana ne ba kome na yafe maka. Haka dai aka sasanta su ka dunguma cikin birni baki daya.

da gari ya waye Sarki ya fito fada ya zauna, boka Sakaradiyyuna na kusa da shi a zaune. Can sai ga Malukussaifi da sa’adunizanji sun shigo, da zuwansu sai Sarki da sauran
jama’a duk suka mike kamar yadda suke yiwa Sa’aduninzanji bayan da su kai gaisuwa gaban Sarki sai duk aka zauna, zaman
su ke da wuya Malukussaifi ya dauko littafin Halwanu ya mikawa Sarki ya ce, “Ga littafin da ake bukata daga gare ni na
kawwo.’

Sarki ya karba ya mikawa boka ya karôa ya ajiye. Aka cigaba da harkokin mulki har lokacin tashi daga fada ya yi duk
jama’a suka watse boka Sakaradiyyuna ya dauki littafi ya
koma masaukinsa yana tunanin to yanzu kuma wane makircin zai sake kullawa Maluussaifi

Bayan da dare ya yi sai boka ya sa aka kirawo masa wasu mutane daga cikin irin ragowar mutanen da Sarki Saifu’ar’adu ya aiko su tare da Manadihulbigali, su ashirin da biyar ne cikinsu dubu suka rage Sa’adunizzanji bai halaka su ba, da zuwan
mutanen gaban boka Sakaradiyyuna suka fadi suka gai da shi,

sannan suka zauna. Boka ya ce da su ya kirawo su ne domin ya
ba su takarda su kai wa babban Sarki Saifu’ar’adu.

Nan da nan ya dauko takarda da alkalami ya fara rubuta takarda ya ce,
Bisimil.zahlu, zuwa ga babban Sarki Saifa’ar’adu, na rubuto
wannan takarda domin na sanar dakai cewa sadaukin nan daka aiko ya nema maka auren yar sarki Afarahu fa, to sarki afarahu dai ya kulla makirici sun hadu shi da sa’aduninzanji da wannan farin yaro daya ajjiye sun kashe manadihul bigali, dan aiken nan naka.

zamu cigaba

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman

Part 3.
kuma idan ma ka sake to wannan farin yaron zai auri Shamatu, wanda ko idan har hakan ta faru-to ba makawa sai ya ture mulkinka, domin kuwa ya samo wannan littafi ma da na
tura shi ya nemo.

Abin da nake so yanzu ka turo sadaukai masu
yawan gaske su zo su yaki Sarki Afarahu da Sa’adunizzanji, da Wannan dan yaro sannan ka mai da Shamatu kuyangarka.

Da ya gama rubuta wannan takarda, sai ya ninke ya mikawa mutanen nan ya ce Wannan ku kaiwa Sarki.” Sannan kuma ya
dauko wannan littafi na Halwanu ya sake mikawa mutanen nan ya ce Wannan kuma ku kula da shi sosai, idan kün je ku baiwa
dan uwana boka Sakaradisa wannan littafi.”

Nan boka ya sallamesu cikin daren suka fice daga garin ba tare da kowa ya gansu ba.
Wannan abu duk ya faru ba tare da sanin Sarki -Afarahu ba.

A kwana a tashi har mutanen nan da boka Sakaradiyyuna ya aika suka isa garin Sarki Saifu’ar’adu. Da zuwansu suka wuce
zuwa fada suka iske Sarki na zaune ana fadanci.

Suka fadi suka
yi gaisuwa gaban Sarki, suka mika wannan takarda ga Sarki, suka kuma mika wannan littafin Halwanu ga boka Sakaradisa.

Nan da nan Sarki ya umarci magatakarda da ya karanta wannan
wasika.Cikin kankanin lokaci ya karanta abin da wannan takarda
ta kunsa, Sarki da wazirinsa Baharu da Boka Sakaradisa duk
suka ji irin abin da Sakaradiyyuna ya rubuta.

Ran Sarki ya baci
hankalinsa ya tashi, ya yi duba ya zuwa Sakaradisa ya ce.Ina dabara?”
Boka Sakaradisa ya ce Idan ba da gasake ka yi ba, to wannan tsinannen farin yaron sai ya karbe wanan mulkin naka
kuma ya mayar da mu bayi, kai hatta tauraruwa Zahlu ma sai va hana mu bautarta.”

Bayan ya gama wannan magana sai ya mikawa Sarki littafin halwanu ya ce, Riki wannan, dan ‘uwana ne ya aiko min da shi

Wanpan shine littafin tarihin Nil Sarki ya karba ya ajiye.
Can shi kuma Waziri Baharu da yake musulmi ne sai ya ce
Wai sakaradisa me ya sa kuka damu da wannan farin yaro bayan a wannan lamari bashi da laifi ai in ma kamawa ne Sarki Afarahu da Sa’adunnizzanji su Sarki zai hukunta a bisa laifinsu kashe Manadihulbigali da suka yi.

Amma shi wannan yaro Kuma da kuke cewa shi ne wanda zai karbe mulkin Sarki, ya aka yi kuka sani, kun san gaibu ne? ai babu wanda yasan gaibu in ban da tauraruwa Zahlu kamar yadda muka sani

Sarki ya ce Haka ne Wazirk, wannan magana taka haka take, babu wanda ya san gaibu in bán da Zahalu, to yanzu Weziri ina dabara bamu shawara.

Ana cikin haka sai wani daga cikin dogarawan Sarki ya
shigo ya gayawá Sarki cewa ga wani tsoho ya zo yana so ya ga
Sarki.

Sarki ya yi umarni da a shigo da shi, nan- da nan aka shigo da da tsohon nan gaban Sarki.

ya fadi ya yi gaisuwa. Sarki ya
tambaye shi, “Me ya kawo ka.”
Tsoho cikin raurawar murya ya ce, Na zo ne na kawo karar shugabanmu gareka, domin ta raba mu da birninmu har ta
kashe wasu da dama daga cikinmu, kuma ta kama ya’yayenmu
da matayenmu suna yi mata bauta,
Ko da Sarki ya ji wannan magana sai ya ce,

Kai mutumin wane gari ne kuma waye wannan shugaba naku, wanda har ya yi
muku wannan ta’adda?”

Tsoho ya amsa ya ce, “Ni mutumin birnin Yemen ne, ni ada na kasance ni ne shamakin Sarki Ziyyazanun kafin ya rasu,
kuma mu duk mutanen kasarmu, mun kasance masu biyayya ga
Sarkinmu.

to yana ciwon ajali kafin mutuwarsa ya yi mana Wasici da cewa, matarsa tana da ciki, idan ya mutu ta cigaba da sarauta bisa gadonsa na mulki har ta haihu. Idan ta haihu dan ya girma ta sauka ta ba shi mulkinsa. Haka muka bi wannan umarni
nasa ba saba ba,

bayan mutuwarsa muka dora wannan mata
mai suna Kamriyya bisa gadon sarauta.

to tun wannan lokaci sai ta fara korar mutanenmu tana jawo
wadansu mutane daban tana ba su mukamai a majalisar kasarmu

Ana haka rannan sai ta haihu da namiji, bayan yaro ya kwana
bakwai ta fito mana da shi fada muka ganshi.

Amma tun daga
wannan rana har yau shi shekara ashirih kénan ba mu kuma ganin yaron ba.

Shi ne na zo na nemi taimako a gareka domin kuwa na ga kai Sarki ne mai girman lamari.”

Ko da boka Sakaradisa ya ji wannan labari sai ya dubi Sarki ya ce, Ai wannen Sarauniya da ake magana ba wata ba ce illa baiwar nan taka Kamriyya, wadda ka ba ta guba ka aike wa da Sarki Ziyyazanun domin ta ba shi ya sha, shi ne ba ta aikata hakan ba ya rike ta a zaman mata, kuma ga shi har ta shekara
ashirin tana mulki amma ba ta aiko maka da haraji wai ita ma
shugaba ce tana gasa da kai ai lallai ne ka yaketa.”

Da jin wannan magana Sarki ya fusata ya ce, Wato wannan tsinanniyyar dai na tura ta ta kashe Sarki Ziyyazanun shi
ne ba ta aikata hakan ba, kuma har ta kira kanta shugaba tana jayayya da ni, to na rantse da Zahlu sai na yake ta na rusa
birninta.”

Waziri Bahru ya ce da Sarki, Ai ba yakar ta za ka yi ba,
domin kuwa ita ma yanzu ta tara sadaukai masu yawa
karkashinta. Ka ga yanzu idan ka tura a yake ta kuma aka je ba
ai nasara ba mutuncinka zai zube a idon sauran sarakunan duniya, a kuma rika cewa ka yaki mace kuyangarka ta gagareka.

Abin da za a yi shi ne, tun da ita Kamriyya ta ki aiko maka
da haraji har tsawon wasu shekaru, to ta saba maka, kuma ga
Sarki Afarahu ya kashe maka dan aike, shi ma ya aikata laifi a
gareka.

To yanzu ka hada su yaki da junansu, duk wanda ya
karya wani mu kuma sai mu rufar masa mu karasa shi. Ka ga
shike nan mun huta.”

Boka Sakaradisa ya yi dariya ya ce, Madalla da wannan
shawara taka, ai kawai ran Sarki ya dade haka za a yi, shi ke nan
Wannan shawara ta yi sarki iya yi na’am da shawarar Waziri, nan da nan ya sa aka
rubuta takarda zuwa ga Sarki Afarahu ya shaida masa da cewa,
Mun samu labari ka kashe dan aikena Manadihu saboda haka ka aikata laifi a gareni. Amma girmanka wajenmu na gafarceka bisa ga abin da ka aikata.

Amma ina so yanzu kaje ka yaki kamriyya sárauniyar yemen, shi ne diyyar da za ka biyani a maimakon Manadihu.”

Bayan da aka gama rubuta wanan takardar aka tashi wani sadauki wanda ake kira da suna Sijiinfili aka hada shi da sadaukai dari uku da dukiya dukiya aka umarce su da su kai wa Sarki
Afarhu wanan takarda da kuma wannan dukiya.

Nan da nan
suka daura surada suka hau suka tafi.

Can kuma Sarki Afarahu hankalinsa ya tashi saboda ya san
idan Sarki Saifu’ar’adu ya samu labarin an kashe Manadihulbigali
a kasarsa kuma babu zancen auren Shamatu da Sarkin ya nena
ko ya san ba makawa sai ya aiko an yaki kasarsa, saboda haka ya
dimauce ya rasa yanda Zai yi.

Bayan wasu yan kwanaki Sijijimfili da sauran jama’arsa suka iso garin Sarki Afarahu. Ko da Sarki Afarahu ya samu
labarin ai ga baraden babban Sarki sun iso kasarsa an aiko su, sai
hankalinsa ya tashi, ya tara yan majalisarsa, cikin su har da
Malulkussaifi da Sa’adunizZanji. Sarki ya ce, To kun ga babban
Sarki can ya aiko Sijijinfiili ya yake mu sakamakon kashe Manadihul bigali.”

Malukussaifi ya dubi Sarki Afarahu ya ce,Kwantar da
hankalinka, mu Za mu fita mu tare shi idan da nufi yake ya zo mana, za mu yake shi mu kashe shi sannan shi ma babban Sarkin
da ya aiko shi mu je mu yake shi.”

Nan da nan sadaukai sukai ta
daura surada suka hau dawaki, Malukussaifi ya shige gaba shi da
Sa’adunizzanji sauran jarumai suka bi su suka fita taryar Sijijiimfili
Ko da Sijjimfili ya hango irim shirin da su Malukussaifi
Suka yi sai ya san lallai sun zata yaki ne ya kawo shi. Sai ya turo

daya daga cikin mutenensa ya zo ya
shaida musu cewa ai ba da yaki suka zo ba kawai an aiko su ne.

Da suka ji wannan bayani sai suka ba Sijjinfili da jama’arsa damar su karaso inda suke da suka zo sai suka hadu suka
dunguma cikin birni, aka sauki Sijijinfili da jama’arsa akai tayi
musu hidima har dare ya yi duk aka kwanta barci.

Bayan da gari ya waye Sarki Afarahu ya fito fada jama’a
duk sun taru ana Jira a ji sakon da Sijijimfili ya ke tafe da shi.

can an nutsu sai Sarki ya ce da shi, Shin menene sakon dake
tafe da kai?”
Sijijimfii ya dauko takardar da Sarki Saifu’ar’adu ya ba shi
ya mikawa” Sarki Afarahu, shi kuma ya karba ya mikawa
magatakardansa domin ya karanta.

Magatakarda ya karanta kowa
ya ji abin da babban Sarki ya rubuto
Ko da Malukussaifi ya ji haka sai ya ce, To ai wannan ma zancen baza ne ya ya wata can ta yi masa laifi shi bai yake ta ba
sannan kuma ya aiko mana wai mu je mu yake ta. a nan
yana nufi kai Sarki a Karkashinsa kake kenan,

to ba za mu yi abin da ya neba ba shi ya zo ya yake ta in kuma ya ji haushi mu
ya zo ya yake mu
Sarki Afarahu ya yi shiru yana tunanin cewa lallai
Malukussaifi da Sa’adunizzanji lallai jarunmai ne na gaske, amma
kuma duk da haka sai ya tuna ai babban sarki Saifa ar’adu yana
da yawan sadaukai jarumai fiye da kima, kuma ya san lallai idan
ya yi fiushi da su duk zai halaka su.

Sai ya dubi Malukussaifi ya
ce, Ya dana, ai ya zama dole mu bi umarnin babban sarki, mu Je mu yaki Kamriyya, idan ku ba za ku ba to ni zan shirya in tafi
da mutanena na yake ta.

Da Malukussaifi ya ji wanan nmagana ta Sarki Afarahu, sai ya
yarda da hakan saboda kasancewarsa mai biyayya a wurin Sarki
domin daukarsa da ya yi Uba a wajensa.

Ya ce,To shike nan mun yarda da wannan magana , za mi bi ka mu je mu yaki
wannan sarauniya ta kasar yemen.

MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN
Littafi na biyu 2
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
rubutawa Shuraihu Usman
Part 4.
.
Bayan wasu yan kwanaki kadan sukai shirin yaki, Sarki
Afarahu da Malukussaifi da Sa’adunizzanji da Sijijimfili da sauran Sadaukai suka fita suka kama hanyar zuwa garin babban
Sarki Saifu’ar’adu, domin su yi gaisuwa da nuna amsa umarni,
sannan su wuce zuwa kasar Yemen su yaki Sarauniya Kamriyya.

Da zuwansu garin babban sarki, sai ya turo aka tarye su aka
kai su fada kowa ya yi gaisuwa gabansa suka zauna ban da
Sa’adunizzanji, shi sai ya yi tsaye yana muzurai ko gaida Sarki
bai yi ba.

Ganin haka sai babban sarki ya dubi Sarki Afarahu ya
ce, Shi kuma wannan waye wanda yake tsaye?” Sarki Afarahu
ya ce, Wannan shi ne Sa’adunizzanji.” Babban Sarki ya ce, To
shin shi ya fiku ne duk kun yi gaisuwa amma shi yana tsaye
Ko da Sa’adunizzanji ya ji wannan magana sai ya fusata ya
ce da babban Sarki, To don me zan gaishe ka, kana zaton ni
talakanka ne, to baka isa na gaishe ka ba.”

Nan da nan sai
jayayya ta balle tsakanin babban Sarki da Sa’adunizzanji, su kai ta yi Can sai boka Sakaradisa ya matsa kusa da Sarki Saifu’aradu ya rada masa ya ce, Ran Sarki ya dade, mai ya kai ka jayayya
da wannan bakin bawan.

Ai in ka biye masa yanzu yaki ya tashi
a nan, ka rabu da shi kawai ya fi”
Sarki ya yarda da wannan shawarar ta boka ya daina jayayya da
Sa’aduniZZanji, ganin haka shi kuma Malukussaifi ya umarci Sa’aduni
da ya zauna, sannan ya zauna.

Akai ta fitowa da abinci iri-iri ana
baiwa jama’a, suka ci suka sha, kai haka dai akai ta yin hidima har
kwana biyu
Bayan wadannan kwanaki sai babban Sarki ya sallame su suka fito
domin su tafi su yaki sarauniya Kamriyya.

A wannan lokacin bayan sun fito sai Malukussaifi ya umarci Sarki Afarahu da ya koma gida shi da
Sa’adunizanji da sauran sadaukai za su tafi wurin wannan yakin.

Sarki Afarahu da rabin mutanen da suka fito suka koma gida, Malukussaifi
da Sa’adunizzanji da sauran sadaukai suka kama hanyar su ta zuwa
Yemen domkn su yaki Sarauniya Kamriyya.

A lokacin da suka je kasar babban Sarki Saifu’ar’adu kafin su fito, bash san ba sai babban Sarkin ya rubuta takarda zuwa ga Sarauniya Kamriyya ya ce,”Zuwa ga sarauniya Kamriyya, na rubuto
miki wanan takarda domin ina so ki biya ni haraji har na iya tsawon
shekarun da kika yi kina mulki.

ldan kuma ba haka Ba rundunar
mayakana suna nan tafe Zuwa gareki Da ya gama rubuta wannan
takardar sai ya aika wa wani dogari ya umarce shi da ya yi maza ya tafi
kasar Yemen ya kai wa Sarauniya Kamriyya.

Bayan yan kwanaki dogarin nan ya isa birnin Yemen da zuwansa
ya wuce zuwa fada a kai masa iso ya shiga ya yi gaisuwa ya fadi sakon Sarki.

Da Kamriya ta karanta wannan takarda sai ta ce da dogarin nan, in ce ko dai shi Sarki Saifi’ar’adu ba shi da hankali ne? Yanzu kamar ni ya ce in biya shi haraji, to ka koma ka gaya masa
ba zan biya shi ba, kuma idan yaki ne zamansa nake.

Kwana biyu da yin wanannan sai Kamriyya ta samu labarin ai ga wata rundunar mayaka nan ta nufo biminta kuma ga yadda labarin ya zo mata ta firgita da jin yadda aka gaya mata yawan su da kuma irin
shirinsu.

Wato wannan runduna ba wasu bane illa Malukussaifi da
Sa’adunizanji da Sijijimfilk da sauran jama’ar da suke tafe da su
kafin magaruba Malukussaifi da jama’arsa suka karato birnin yemen suka hangi katangar birnin an gina ta da farin dutse da manya manyan kofofi na jan karfe.

A nan sai ya umarcesu da su sauka
a nan su kwana, gari na wayewa su auka cikin garin da yaki, nan duk
aka sauka aka kafa rumfuna na tanti, duk suka saki dawakinsu domin
Su yi kiwo su kunma kowa ya shiga rumfarsa ya kwanta aka bar wasu suna
gadi
Can bayan an natsu cikin dare sai Kamriyya ta hau doki ta sulalo
ta fita daga cikin birni ta nufo inda su Malukussaifi suke.

Da Zuwa da sai ma su gadun nan suka tare ta suka tambaye ta ina za ta,
ta ce da su ai ite lallai shugabans take so ta gani nan da nan aka
je aka gaya wa Malukussaih cewar ga wani mutum ya fito daga
cikin birnin nan ya ce lallai kai yake so ya gani ya ce ku je ku ce
da shi ya koma gebe ya dawo. suka komo suka gayawa kamriyya amma sai ta ki ta dage, ta ce ta lallai sai ta gan shi, suka koma suká sake
gaya wa Malukussaifi, sai ya ce a shigo da shi, aka shigo da
Kamriyya duk
suka fita suka barsu su biyu a cikin tanti.

Malukussaifi ya ce, Me ke tafe da kai?” Kamriyya ta bude
fuskarta ta ce, “ba namiji ba ne, ni mace ce kuma ni ce Kamriyya
Sarauniyar wannan birnin da kuka kawo wa yaki. Abin da ya kawo ni shi
ne, na ga rundunarka tana da karfi kuma ni ma tawa rundunar tana da
karfi, sai na ga in mu kai yaki za a zubar da jini sosai, shi ne na
zo yanzu mu yi kokawa ni da kai duk wanda ya yi nasara a kan dayan to
shike nan ya ci shi da yaki, ba sai an gwabza a filin daga ba.

Da ya ji wannan magana tata sai ya ki ya ce sam shi ba zai yi
kokawa da ita ba, tana mace shi yana namiji. Haka dai sukai ta jayayya
har ta shawo kansa ya yarda za su yi kokawar.
Kamriyya ta cire duk kayan dake jikinta ta tsaya daga ita sai
wata riga doguwa mai shara-shara, wadda duk ana ganin halittar
jikinta.

Ita ta yi haka ne domin ta yaudari Malukussaifi ya kamu da
sha’awarta ta samu ta yi galaba da shi. Shi kuma da ya ga haka sai ya
ce bai yarda ba, ba zai yi kokawar a haka ba, sai ta sa kayanta. Ta rika kawo masa wabta yana gocewa har ta yaga masa riga ganin haka shi
kuma sai ya fusata ya cire rigarsa, yana Cirewa sai Kamriyya ta ga
sarkar nan da ubansa ya ba ta kafin ya mutu ya ce in ta haihu ta
rataya wa dan a wuyansa.

Tana ganin haka, sai jikinta ya yi sanyi ta tambaye shi inda ya
samu wannan sarkar ya gaya mata, ya ce shi dai tashi ya yi ya ganta
a wuyansa tun yana karanmi. Nan da nan ta ce, Wallahi kai dana ne,
duk inda a kai kai dana ne, domin kuwa wannan sarkar asalinta ta
ubanka ce Sarki ziyazzanun.

Kafin mutuwarsa ya bani ita ya ce idan
na haihu na rataya wa dan da na haifa a wuyansa, shi ne da na haife
ka na rataya maka i ta, kuma tana wuyanka na je far da kai a daji. Ni ce uwarka.”

Malukussaif ya ce ai shi bai yarda ba, ya za ai in dai uwar tasa ce ita ta yada shi, Sukai ta jayayya can sai ya ce, To na ji.

yanzu meye kuma shaidar ki bayan wannan Ta ce.akwai shaida, zan koma cikin birni zan zo da irin yaran ubanka domin su yi maka
shaida.”
Nan da nan Kamriyya ta koma cikin birni ta kirawo wasu tsofaffi
su hudu wadanda suka rage daga cikin yaran Sarki Ziyyazanun, ta taho
da su gurin Malukussaif ta ce da su, Ku raba mana wannan gardarmar,
ni na ce dana ne, shi kuma ya ce ba shi bane.”Tsofaffin nan suka
dube shi suka ga yar alamar nan dake kundukukinsa (kumatunsa kenan),
sai suka ce, lallai babu shakkar cewa danta ne,”Shugabanmu ne kai,
mun rasa ka yau tsawon shekara ashirin da daya.”
Nan dai har sai da Malukussaifi ya gasgata su ya san lalai
Kamriyya uwarsa ce ba aljana ba ce uwarsa.

Sai ya ce da ita, Ke
kuwa me ya sa kika yadda ni kina mahaifiyata?” Kamiyya ta fashe da
kuka, ta zare takobinta ta mika masa ta ce, dana, karbi takobin nan
ka yanka ni, domin ka rama abin da na yi maka, domin ni yanzu burina
na duniya ya cika tun da na sake saka ka a idona. Yimaza ka yanka ni
ka shiga birninka, kaci gaba da mulki.

“Malukussaifi ya rungume ta
yana hawaye yana cewa, Ki yi
shiru ba komai.”

Bayan haka sai Kamriyya ta ce, Ai sai ka kwana a nan, gobe da
safe za mu fito ni da jama’ar gari baki daya.

Mu zo mu tarye ka mu
shigar da kai garinka, in baka mulkinka.” Sukai sallama Kamriyya da
tsofaffin nan suka koma cikin birni.

Da komawarsu ta bai wa tsofaffin
nan abinci da guba suka ci duk suka mutu, babu wanda ya san abin da
ya faru, ta zauna tana bakin ciki tana cewa a zuciyarta, “Ka ga
shegen yaron nan da na jefar da shi don ya mutu saboda kada ya karbe
mulki na, ashe bai mutu ba ya
dawo.

Haka dai ta zauna tana ta tunanin makircin da za ta sake kullawa
danta Malukussaifi. Can sai dabara ta zo mata, ta tashi ta hau doki
cikin wannan daren ta kuma komawa bayan gari wurin Malukussaifi.

Da Zuwanta a kai mata iso ta shiga ta ce, Ya dana na dawo.
Abin da ya dawo da ni shi ne, na z0 ne domin na faiyace maka dukkan yanda lamarin ya faru a baya.

Ni na kasance na kan sami tabin hankali wani lokacin,
Wani lokacin ka ganni da hankali. Lokacin da na yadda kai ba nida
hankali, a wannan lokacin ban san abin da nake ciki ba. Na ki gaya
maka ne dazu saboda ganin wadannan mutane da na zo da su.
Abu na biyu kuma shi ne, ubanka ya bar maka dukiya mai yawan
gaske, saboda gudun kada wasu daga cikin Sarakunan duniya su kwace
maka ita sai na debi mutane muka dauki dukiyar muka tafi can dan
daji muka binine ta. Bayan mun binne wannan dukiya, mulanen da na je da su
sai na kashe su, yanzu duk duniyar nan babu wanda ya san inda wannan
dukiya take sai ni. Saboda haka yanzu tashi mu tafi in nuna maka
dukiyarka.”

Bai yi musu ba ya tashi ya bita suka hau dawaki suka kama hanya
sukai ta tafiya cikin daren nan, har gari ya waye rana ta fito suna ta
tafiya subiyu cikin daji har rana ta tafi. Kai haka dai sukai ta
kutsa kai cikin daji su biyu har kwana uku.

A cikin wannan hali duk
lokacin da dare ya yi sai ta kwanta ta yi barci shi kuma ya tsaya yana
gadinta har sai ta farka, sannan su ci gaba da tafiya. To a wannan
rana ta uku sai barci ya kama Malukussaifi, mahaifiyarsa ta ce, To
yau kai ma ka yi barci ni kuma na yi gadinka.”

Malukussaifi ya kwanta ya tada kai da cinyar mahaifiyarsa ya fara
barci. Cikin kankanin lokaci sai ya fara minshari, barcinsa ya yi
nisa. Ko da Kamriyya ta fahimci ya yi nisa cikin barci, sai ta zame
jikinta a hankali ta tashi ta dauko wata Gariyo (wuka) mai guba ta
dubi kan Malukussaifi ta kafta masa sara jini ya yi tsattuwa sama, ta kuma saransa a wuyansa, ta sake saransa a kirji, sannan ta yanke shi a ciki.

Ta juya ta hau dokinta ta tafi ta barshi cikin jini
kwance, tana zaton ta kashe shi. Haka ya kasance cikin wannan hali har asuba ta yi, sanyin asuba
ya buge shi ya farka daga suman da ya yi.

Malukussaifi ya ga duk
jikinsa jini ya yunkura zai tashi amma sai ya kasa saboda gubar dake
jikin gariyon nan ya shige Shi nan sai ya yi addu’a ya roki
Ubangiji da ya kawo sababin da zai kubuta daga wannan hali da yake
ciki. Yana rufe bakinsa sai ya ga wasu tsuntsaye guda biyu sun zo sun sauka akan wata bishiya da take kusa da shi.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*