FARATAN ZAKI littafi na daya 1 Part D

FARATAN ZAKI
Littafi na daya 1
na Shuraihu Usman
Part D
.
sarki huntaru ya sauke ajiyan zuciya bayan gama sauraran labarin muzaffar ya dubi muzaffar ya ce “hakika kam kamar yadda boka balbalin bala’i ya sanar dakai cewa duk duniya babu wanda yasan inda taswirar zuwa kogon zakuna yake, haka batun yake, sai dai a shekarun baya manyan matsafa da bokayen duniya sunyi zama inda suka hada karfi da karfe wurin ganin sun binciko inda taswirar take amma sun gagara, kai daga karshe ma sai da rabinsu suka hallaka daga cikin wayanda suka tsira akwai wani hatsabibin boka mai suna dundamu, boka dundamu shine kadai ya iya gano inda taswirar kogon zakuna yake. “

cikin Zakuwa muzaffar ya ce “ina ne taswirar take”
sarki huntaru yayi murmushi ya ce “ka kwantar da hankalinka ya namijin kwarai, da sannu zan sanar dakai abunda ka ke bukatar sani “
sarki huntaru ya dau ruwan inibin dake gaban muzaffar ya kwankwada bayan ya kwankwada sai ya fara baiwa muzaffar labari kamar haka “kamar yadda na sanar dakai a baya boka dundamu yayi nasarar gano inda taswirar kogon zakuna yake, kamar yadda bokayen Attajiri Almadud suka shara’anta cewa taswirar ba zai bayyana kanshi ba sai ga ahalin almadud, to bayan kimanin shekaru dubu biyu, a can yankin bakaken fata a taswirar ta bayyana a cikin birnin Burkatus Aswad.

shidai birnin burkatul aswad na karkashin mulkin wata sarauniya ce wacce bata kasance bakar fata ba mai suna Badariyya, ita dai badariyya ta kasance daya daga cikin tsatson Attajiri Almadud. sarauniya badariyya ta kasance yar kasar hindu ce, sarkin Burkatul Aswad ne mai suna Marutu yaje har birninsu ya auro mahaifiyarta, ya kuma zauna a birnin na hindu har sai da mahaifiyar Sarauniya badariyya ta haihu sannan ya kamo hanyar dawowa kasarsa.

bayan Rasuwarsa ne Yarsa Sarauniya Badariyya ta haye kujeran sarautarsa ta cigaba da shimfida mulki, gwargwardon yadda mahaifinta yake, ta tsayu bisa ga talakawanta tana aikatawa garesu aikin alheri, har wata rana Taswirar Kogon zakuna ya bayyana gareta cikin dare.

yayin nan tana kwance cikin turakarta sai tayi mafarki a cikin mafarkin taga Wani tsoho fari sol yana haye bisa doki na zinare sannan ga mutane nan birjik a zagaye da tsohon dukkansu suna tafe bisa dawakan da aka sana’anta da zinare. yayinda tsohon ya kariso gareta sai ya sauko ya nufota ya ce “Lale marhaban da jikata Sarauniya badariyya cewa ni ne kakanki Attajiri Almadud mafi daukaka da arziki daga dukkan sarakuna da attajiran duniya, yake jikata hakika ni na adana gareki dukkan dukiyata na daga dangin zinare,lu’u lu’u,jauhari,zubardaji da yakutu hadi da dukkan hadimaina na Aljanu.” tsohon na zuwa nan a zancensa ya dauko wata jan takarda daga aljihunsa da aka sana’anta da ruwan zinare.

ya mika wa sarauniya badariyya ya ce “riki wannan taswira ya jikata, itace zata sadaki da kogon dana adana dukiyarki, kuma a tare da wasikar nan akwai manyan hadimai na Aljanu da zasu jagoranceki zuwa ga kogon zakuna” sarauniya badariyya ta amshi taswirar daga hannun almadud, fuskarta cike da mamaki ta ma kasa furta koda kalma daya, a haka Tsohon ya juya yaje ya haye bisa ga dokinsa na zinare ya juya shida sauran mutanen dake tare da shi.

Sarauniya badariyya na zuwa nan a mafarkinta sai ta farka firgigit, ta na dube dube. koda ta tsinci kanta bisa ga luntsumemen katifarta sai ta sauke ajiyar numfashi ta sakankance mafarkine tayi. tana shirin ta koma ga kwanciyarta kenan idanuwanta suka sauka kan abunda yai matukar bata mamaki, ba komai ta gani ba face wani Jan takarda abun sana’antawa da zinare yana sheki da daukar idanu, hasalin abun mamakin ma shine takardar yana bisa kan iska ne baya sama kuma baya kasa.

Sarauniya Badariyya ta nufi wannan takarda cikin mamaki da al’ajab ta dau takardar, ta iske babu komai cikin takardar face wasu zanuka da bata gane ko zanen mene ne ba. nan da nan sai mafarkin da tayi ya fado mata a rai ta sakankance wannan taswira itace wannan dattijo ya mika mata.

tana a cikin wannan hali ne, wani aljani daga dangin fararen al’janu ma’abocin kyawun sura ya bayyana gareta yana mai dukawa kasa ya gaisheta ya ce “ya shugabata hakika ni nakasance daga cikin bayin kakanki Attajirin duniya Almadud kuma ya umarceni dana damka wannan taswira ga hannunki, cewa wannan taswira ita zata jagoranceki ga bigiren da mahaifinki ya adanta dukiyarsa mai tarin yawa da baki bazai iya fadan yawansu ba.”

sarauniya badariyya ta ce “kai kuwa ya ya sunanka sannan ni nakasance cikin bata da wannan al’amari daya ke gudana gareni”

Aljani ya ce “, Suna na Harijul Burkatu ni ne sarkin fararen Aljanun duniya baki daya kuma ni na kasance bisa da’arki cewa ki shugabata ce” A nan Aljani Harijul Burkatu ya kwashe dukkan labarin Attajiri Almadud da yadda ya taskance dukiyarsa a bigiren da babu wanda ya sani.

sarauniya badariyya ta yi mamaki ainun da labarin da Aljani Harijul burkatu ya bata ta sake duba taswirar Kogon zakuna tana tu’ajjibi.

tun daga wannan rana sarauniya Badariyya ta taskance Taswirar kogon zakuna a tare da ita. ya zamana ta sanya madinki ya nade ta ya mayar da ita laya ta rataya layar bisa wuyarta.
Bayan Sarauniya Badariyya tayi aure ta haifi ‘ya mace kyakkyawa ta gaban kwatance wadda masana da bokaye suka yi ittafakin duk duniya babu mai kyawunta. sarauniya ta sanya wa yarta suna Zatal dawahi sannan ta cire layar nan daga wuyarta ta sanya bisa ga wuyar yarta.

*** *** ***
shi ko al’amarin boka dundamu bayan yayi nasarar gano inda taswirar kogon zakuna take sai ya isa ga bigirenshi dake can gabashin birnin sin a wani tsibiri mai suna Tsibirin Jauhari.

boka dundamu yayi gagarumin shirin tunkarar Sarauniya badariyya da nufin kwatar Taswirar kogon zakuna daga hannunta, bayan ya gama shirinsa ya fasaltu da irin shigar Bokaye wanda muddin mutum yai arba dashi sai ya girgiza, nan take ya bace bat daga kogon tsafinsa.

boka dundamu bai bayyana a ko ina ba sai a bayan birnin Burkatul Aswad inda sarauniya Badariyya ke mulki, to dama su mutanen burkatul aswad sun kasance bisa tafarkin ibrahimiya ne wato su musulmai ne. bayan da boka dundamu ya bayyana a bayan birni sai ya juye kamaninnsa ya zuwa kamilin dattijo sanye da shiga ta kamala ya shiga cikin birnin, kai tsaye bai wuce ko’ina ba sai fada inda ya iske Sarauniya badariyya na bisa kan karagar mulki, ga yarta Zatal dawahi a gefenta. a wannan lokaci zatal dawahi na da shekaru goma sha tara. in ka gansu a hakan sai ka zata watanni ne, dattijo ya fadi gaban Sarauniya yayi gaisuwa sarauniya ta tambayeshi me ke tafe da shi.”

boka dake cikin suffar dattijo kamilalle ya ce ” yake sarauniyarmu mai adalci da karimci wata musiba ce ta afka gareni na rasa dana daya tilo dake taimakamini a bisa ayyukan gona, kuma gashi tsufa ta riskeni bana da isasshen karfin da zan iya wani aiki”

yayin da sarauniya taji kalaman dattijo sai tausayinsa ya shigeta, ta dubi sarkin fada dake gefenta ta ce ” ya Mas’udu ka tafi da wannan dattijo izuwa ga taska ya debi dukkan abunda yake bukata na daga dirhami sannan akai buhun hunan hatsi dubu gidansa.”

Sarkin fada ya ce ” Naji na kuma bi ya shugabata” nan da nan ya mike ya dubi dattijo yace ” muje”. dattijo ya mike sai ya faki idon kowa yayi wuf ya nufi zatal dawahi ya kai hannu wuyanta da nufin fincikar layar dake wuyan nata, ai sai yaji hannunsa ya makale a wuamyar zatal dawahi gashi dai ya damki layar amma ya kasa sarrafa hannunshi, Sarauniya badariyya da sauran Fadawanta da dakarunta suka mike zumbur ind sarkin yaki Afaladinu ya zare takobinsa ya datse hannun boka dundamu dake rike da layan zatak dawahi.

boka yayi ihu yayi kururuwa saboda zogi da zafin da suka ziyarce, Sarkin yaki sake kawo masa sara karo na biyu da nufin datse kansa ganin haka boka dundamu ya ambaci wasu kalaman tsatsuba ya bace bat.

tsulum ya bayyana Bigirensa dake Tsibirin Jauhari cikin kogon tsafinsa nan da nan. ya fara ambaton kalaman surkelle yana hamhama yana dandama bakinsa na fidda hayaki, a haka ya wanzu yana mai ambaton dalamisan tsafi har bayan watanni biyu, to asannan ne guntulallen hannunsa ya tsiro da kansa, ka ce shi yakasance tushen bishiya ce.

Boka dundamu yayi bincike a halwar tsafinsaa ya gano cewa duk duniya babu wanda ya isa ya taba wannan layar dake wuyan Zatal dawahi sai ire iren zuri’ar Attajiri Almadud, hasalima an sana’anta wani dako da baya barin kowa ya taba taswirar fa ce Jinin attajiri almadud. yayin da boka dundamu ya gano wannan lamari a halwar tsafinsa sai ya takarkare ya kwarara ihu dayai amsa kuwwa a gaba dayan fadin tsibirin jauhari sannan ya fashe da kuka ganin burinsa na mallakar Dukiyar Attajiri Almadud baza ta cika ba.”

bayan da sarki huntaru ya zo nan a labarin da yake baiwa Muzaffar sai ya dada daukar tambulan na ruwan inibi ya kora ya ce ” to kaji labarin Tasiwirar kogon zakuna, da kuma inda yake ni yanzu zan fita na dawo gobe nai maka rakiya izuwa yankin kasata”

sarki huntaru ya fice daga turakar ya bar muzaffar cikin tunanin ta yadda zai sadu da Tasiwarar kogon zakuna don isa can kogon ya yaki sarkin zakuna ya ciro farcensa ya kawo aiwa dan uwansa magani…

Anan na kawo karshen littafi na daya 1 Muhadu a littafi na biyu don jin sauran labarin.
Naku Shuraih Usman – 08140419490 ke cewa na barku lafiya cikin koshin lafiya…

© Shuraih 99% – Hausaebooks 2020

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*