FARATAN ZAKI littafi na daya 1 part C

FARATAN ZAKI
Littafi na daya 1
na Shuraihu Usman
Part C

Sarki huntaru na karisowa gaban muzaffar sai ya tsaida dokinsa sannan ya sauko daga kan dokin ya durfafi muzaffar cikin takun kasaita, koda isowarsa gaban muzaffar sai ya rungune muzaffar a jikinsa yana mai cewa “lale marhabun da gwarzon jarumi cikamakin sadaukai, yarima muzaffar ibn Azlam, wanda ya ya baro birnin Marhabur Sihir don zuwa kogon Almadud a bisa lalurar dan uwanka kuma Amininka Yarima Rabbasu ibn Zurkimu”

Muzaffar yayi mamaki da yadda akai sarki huntaru yasan al’amuransa ya ce ” yakai wannan sarki shin taya akai ka sanni har ma kasan dan uwana da abunda ya afku gareshi da kuma inda na nufa”

sarki huntaru najin haka ya babbake da dariya mara dadin sauraro ya ce “hakika Al’amuranka sun bayyana gareni cikin sha’anin tsafina tun gabanin zuwanka wannan birni nawa, yakai muzaffar kayi sani cewa ina dauke da kyakkyawan albishir a gareka, cewa ni nayi sani da inda aka taskance Taswirar Kogon Almadud da akewa lakabi da kogon Zakuna.”

Koda muzaffar yaji ce wa sarki huntaru yasan inda taswirar zuwa kogon zakuna take sai ya fadada fuskarsa da murmushi ya ce “Yakai wannan sarki mai ababen mamaki da al’ajab kai ko ya akai kasan inda aka taskance taswirar kogon zakuna alhalin manyan bokaye sun tabbatarmin da jinin Almadud ne kadai yasan inda taswirar kogon zakuna yake shin kai jinin Attajiri Almadud ne”

sarki huntaru ya ce “ko da ya ni bankasance jini daga zuri’ar attajiri almadud ba, amma nayi sani da abubuwa da dama da suka jibance shi, yanzu dai ina baka hakuri abisa abunda jama’a ta sukai maka sannan ina mika gayyata ta a gareka da mutafi izuwa fadata ka huta kaci abinci daga nan na sanar dakai dukkan wasu abubuwan da kake bukatar sani gameda Attajirin Duniya Almadud.

Muzaffar yabi sarki huntaru da rundunarsa suka karasa fadarsa, bayan sun isa fadar ne sarki huntaru ya sanya aka baiwa muzaffar babban Masauki inda ya saba saukan manyan mutane masu daraja.

koda muzaffar ya yi wanka ya huta gajiyar da ke jikinsa, aka gabato mai da abinci kala kala na daga dangin kayan lambu da ababen sha nadaga ruwan inibi, sai a sannan yunwar muzaffar ta motsa ya gabato gaban abincin da nufin faraci nan take sai ya tuna da gargadin da dattijo yai masa.

ya fasa cin abincin yaje ga jakar guzurinsa ya duba ko zaiga ragowar abincinsa, ya tarar da jakar babu komai a ciki, abunda ya bashi mamaki kenan domin kuwa ya taho da naman barewa a cikin jakar tasa.

yana a cikin wannan haline sarki huntaru ya shigo cikin turakar ya tarar da shi, sarki yai dubi ga tarin kwanukan abincin dake gabansa yaga ko daya ba’a taba ba ya dubi muzaffar ya kauda kai, muzaffar ya mike tsaye zumbur yai gaisuwa gareshi sannan sarki huntaru ya zauna kusa da muzaffar ya ce “tun da ka huta kuma ka kimtsa cikinka da abinci, to ina saurarenka me kake son sani daya danganci Almadud da Kogon zakuna”

muzaffar ya numfasa ya ce “Na baro gida ne bisa wata lalura ta rashin lafiya data afkama dan uwana, yarima Rabbasu na shanyewar barin jiki, kuma bokaye sun tabbatarmin da cewabba zai taba warkewa har sai naje kogon zakuna, na samo FARATAN kafar sarkin zakuna na kogon, na mikashi garesu domin hada wani maganin da zai warkar da dan uwana, wannan yasa nayi shiri na baro gida na nufi wurin wani hatsabibin boka a nahiyarmu mai suna Balbalin bala’i, koda na isa ga boka bal balin bala’i na sanar da shi bukatata na zuwa kogon zakuna sai ya kwantsama kara mai firgitarwa ya tumu da kasa ya dubeni ya ce ” kai yaro karyarka tasha karya, baka isa ba kuma baza ka isa ba”.

yayin dana ji kalaman boka bal balin bala’i sai raina ya harzuka na dubeshi da duba irin na jarumai na daka masa tsawa na ce “karyane, ni Muzaffar dan Azlam naci alwashin sai na isa ga kogon zakuna na idda bukatata na kashe sarkin zakuna na yanko faratansa don aiwa dan uwana magani, na rantse da taurari ababen sheki a cikin duhu, duk wanda ya shiga tsakanina da wannan buri nawa sai na sada shi da ajalinsa”

boka bal balin bala’i ya tsayu a gabana yana saurarona bayan na idda ya ce “hakika naga kafewa da zuciyar jarumta a tattare dakai samari amma ina mai baka shawara daka koma gida kayi zamanka ka more sauran ranakun da suka rage wa dan uwanka kana tare dashi, domin kuwa Matsafa, bokaye, Attajirai, jarumai da saudaukai bila haddin sun rasa rayukansu bisa wannan tafarkin naka. yakai wannan saurayi kayi sani cewa duk duniya babu wanda ya taba zuwa kogon zakuna ya dawo a raye hasalima duk duniya a yanzu babu wanda yasan inda kogon ya ke.”

koda muzaffar yaji haka sai ya mike tsaye ya ce “Nayi rantsuwa da taurari gamida cin alwashi a wannan fita tawa bazan koma gida ba sai da FARATAN ZAKI, koda kuwa zan rasa rayuwata, sai de na rasa bisa bukatata, nazo ne gareka dun ka taimakeni ka dora ni bisa hanya.”

Boka balbalin bala’i shima ya mike tsaye ya dafa kafadar muzaffar ya ce “an gaisheka jarumin jarumai NAMIJIN GASKE, kwarin guiwarka ta burgeni a sabida haka zan sanar dakai yadda zakai ka isa kogon zakuna, kamar yadda na sanar dakai a baya yanzu a wannan zamani babu wanda yasan inda kogon zakuna yake a wannan duniyar, shekaru dari uku da suka shude ne aka samar da kogon zakuna ta hanyar alkaluman tsafi, sannan an sana’anta wata taswira wadda zata sada mutun ga kogon, wannan labari dana ke baka kakana ne ya sanar dani kuma yana daga cikin bokayen da suka sana’anta kogon zakuna, kuma a yanzu a wannan zamani da muke ciki babu wani wanda yasan labarin tasiwirar kogon zakuna in ba ni ba.

kakana ya sanar dani cewa alokacin nan Attajiri Almadud Mafi daukaka da arziki daga dukkan attijiran duniya, yayi nufin ya taskance tarin dukiyarsa da ya mallaka a duniya wayanda yawansu bazai fadu ba kuma bazai misaltu ba, Awancan zamanin Almadud ya mallaki zinariya, lu’u lu’u, zubarjadi,yakutu fiye da dubu zambar bisa dubu zambar, ance a lokacin nan nahiya guda aka kebance aka zuba dukiyar attajiri Almadud. azamanin attajiri almadud ya juya duniya a tafin hannunsa domin ko yana da dakaru dubu zambar bisa dubu zambar daga jinsin mutane da aljanu.yayin da ajali ya kusanto wa attajiri almadud sai ya kebe da bokayensa su dubu dari shida ya sanar da su cewa “yaku manyan bokayena kuma dirakun dake rike da dukkan kadamina, kun sani cewa na mallaki dukiya mai yawa wadda ni kaina bansan adadinta ba, hakanan gashi ajalina ya kusantoni, kuma gashi haryanzu bana da magajin da zan iya barin masa wannan tarin dukiya tawa, lallai nayi sani muddin akace babu ni na mutu to tabbas al’umma da dama zasuyi kokarin mallakar dukiyata wanda hakan zai jawo ZUBDA JINI a bankasa. ko kadan bana bukatar wani abu makamancin haka ya faru ta dalilina don haka na zo gareku domin ku sana’anta mini wani kogo bisa ilimin alkaluman tsafi da zan ajjiye dukiyata a ciki, yadda babu wani dan adam ko Aljanin da zai iya isa gareta. don gujewa zubar da jini a ban kasa”

yayin da bokayen nan su dubu dari shida sukaji jawabin Attajiri almadud sai shugabansu ya gabato gaba ya ce “ya shugabana hakika abunda ka fada na daga dukiyarka gaskiya ce nan gaba, al’ummar duniya zasu riga kokarin mallakar dukiyar ka wanda hakan zai jawo mummunan zubda jinin da ba’a taba irinsa ba a tarihin duniya. sai dai ka sani ya shugabana Bayan mutuwarka da watanni hudu matarka Zulfulaifa zata haifi ‘ya mace, amma ita kanta yartata baza ta samu koda dirhami guda na daga dukiyarka ba. bisa bincikena na gano cewa tsatsonka na nan gaba sune zasu mori dukiyar, zasu ketare duk wani hadari su isa ga kogon da zamu boye dukiyar inda kuma a karshe zasu mallaki dukiyar taka.”

Attajiri Almadud yayi farin ciki da jin cewa bayan mutuwarsa matarsa zata haihu, amma kuma yayi bakin ciki kasantuwar bazai samu dman ganin jaririyar ba hakanan yar tasa bazata mori komai daga dukiyarsa ba. nan da nan ya baiwa bokayen umarni da su sana’anta KOGON ZAKUNA.

sai da bokayen suka shafe shekaru uku cur suna aikin sana’anta kogon sannan suka iddar, suka aikata aikin sihiri bisa alkaluman tsafi suka samar da zakuna sama da dubu zambar a cikin kogon, kuma suka shafe kogon daga ban kasa tayadda babu wani mutum ko aljan daya isa ya gano ind yake. sai dai bokayen sun sana’anta Taswirar kogon wanda suka killaceta acan wani wuri wanda babu wanda ya sani. sannan suka sake aikata wani aikin sihiri wanda nan gaba taswirar zai bayyana kansa ga jinin Attajiri almadud.” koda boka balbalin bala’i yazo nan a zancensa sai y dubeni yace “to saurayi kaji iyakacin abunda na sani gameda Kogon zakuna, kuma wannan bayanin dana sanar dakai a yanzu haka duk fadin duniya babu wanda ya sani sai ni dakai”
daga nan na sallami boka balbalin bala’i na kamo hanya zuwa ga muradina na cigab d tafiya dare da rana har na iso wannan birni naka ” Muzaffar na zuwa nan a zancensa ya kai hannu ya dau kofin inibi zai bakinsa sai kuma ya fasa ya ajjiye ya ce “yakai wannan sarki kaji dukkan labarina, yanzu kai nake jira ka sanar dani inda Taswirar kogon zakuna take”…

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*