FARATAN ZAKI littafi na daya 1 Part B

FARATAN ZAKI
Littafi na daya 1
na Shuraihu Usman
Part B

Sai da muzaffar ya shafe kusan kwanaki talatin yana keta daji batare daya gamu da wani abun cutarwa ba.

a kwana na talatin da daya ne yana kan tafiya sai ya hango wani tsoho kwance cikin jini ga wata jibgegiyar kure na yunkurin far masa,

koda muzaffar yaga abunda ke shirin faruwa ga dattijon nan kuma yaga muddin kuren nan ya kariso gareshi labudda sai ya kasheshi cikin zafin nama muzaffar ya dako tsalle daga kan dokinsa ya dira a gaban kuren, daidai lokacin da kuren ya yi tsalle zai farwa dattijon nan.

kwatsam sai muzaffar ya dire a gaban tsohon kuren ya fado a jikinsa, muzaffar ya daga kuren da iyakacin karfinsa ya maka da kasa, kuren ya mike a fusace yana gurnani yana kallon muzaffar kafin ya yi sake yin tsalle a karo na biyu ya fada kan muzaffar suka kaure da kokawa, kuren na kokarin sanya hakwaransa ya farke wuyan muzaffar, shi kuma muzaffar na kokarin sake daga kuren ya maka da kasa.

suna cikin kokawanne Muzaffar ya zaro wata karamar wuka daga kuibin cinyarsa ya luma wa kuren a wuya, kuren yayi ihu gamida yin gefe jini na zuba daga wuyarsa. daga nan ya gudu cikin daji

muzaffar ya juyo wurin da dattijo ke yashe a kasa ya sameshi jina jina, cikin halin mutuwa cikin sauri ya tsuguna ya tallafo kan dattijon sannan ya dauko salkar ruwansa ya kafa wa tsohon a baki, tsohon ya ture salkar ruwan daga bakinsa ya dubi muzaffar yace cikin shakakkiyar murya “yakai wannan sadaukin saurayi, hakika kayi niyyan cetona daga sharrin kuren nan amma bakin alkalami ya bushe, domin ko shakka babu nasan mutuwa zanyi amma kafin na mutu ina son na sanar dakai cewa nan gaba kadan zaka riski wani birni mai suna Lamfur, su mutanen wannan birni suna da wata dabi’a na ciyar da bako da zarar ya sauka a garinsu ina horonka da kada ka yarda ka ci ko kasha daga dukkan abun da zasu baka, domin kuwa mutanen birnin Lamfur sun kasance suna bautan wani shedanin aljani ne mai suna Hurratu, kuma a kowanni kwanan duniya suna yanka wa aljani hurratu bil’adama yasha jininsa, hakan yasa duk lokacin da bako ya sauka a birnin suke baibayeshi da abinci wanda suka tsafance, da zarar mutum yaci wannan abincin nasu zai fadi sumamme, daga nan zasu daukeshi su kaishi wurin da suke ajjiye mutanen da suka kama,” dattijon ya dakata ya yi doguwar nishi kafin ya cigaba “da zarar ka shiga birnin to kada ka sake kaci wani abu acikin birnin har sanda zaka fita, muddin ka kiyaye hakan to labudda zaka tsira daga sharrin Al’ummar Lamfur” tsohon na zuwa nan a zancensa rai ya yi halinsa.

muzaffar ya haka rami ya binne gawar dattijon nan sannan yaci gaba da tafiya,

Bayan ya shafe kwanaki biyu yana tafiya sai ya iso birnin lamfur, ya hangi kofar birnin babu masu tsaro, cikin dakewa da yarda dakai ya shiga cikin birnin,

da shigar muzaffar cikin birnin sai yayi arba da yaro karami dauke da akushi akansa, yaron na karisowa gaban muzaffar ya ce “yakai wannan matafiyi barka da shigowa birnin lamfur ma’abociya ni’ima, cewa ni shugabana ya umarce ni dana tsayu a anan wurin duk wanda ya shigo cikin birnin nan na ciyar da shi daga akushin dake kaina,” yaron na gama fadin haka ya miko wa muzaffar akushi.

Muzaffar ya sauko daga kan dokinsa ya amshi akushin yai duba ga cikinsa, yai arba da gurasa da zuma, muzaffar ya manta gargadin da dattijo yai masa ya sanya hannu ya dau gurasar nan da nufin ya kai bakinsa, nan take sai ya tuna da gargadin da dattijo yai masa, ya tsaya cak da gurasar a hannunsa ya kasa kai gurasar bakinsa ya kuma kasa yar da ita, daga can sai ya ajjiye gurasar a cikin akushin ya mikawa yaron akushin ya ce “nagode sosai bisa wannan kyauta taka, yakai wannan yaro, sai de sam ba zan iya cin abincin nan ba”

yaro ya bude baki cikin mamaki yace “kai ko ina dalilin kin cin abincin nan naka, cewa kai ka kasance matafiyi daya shafe kwanaki yana tafiya babu abinci sannan yanzu an gabato ga abinci gareka kana kaki ci”

muzaffar yayi murmushi sannan ya dafa kan yaron bai ce da shi komai ba sai ya wuce abunsa ya shiga cikin gari,

duk inda muzaffar yabi a cikin birnin lamfur sai mutane su rika yi masa tayin abunci, shi kuwa yana ce wa ya gode,

ai koda mutanen Lamfur suka ga Muzaffar yaki cin abincinsu sai suka fusata suka taru suka rufar masa da nufin suyi masa na karfi su ciyar da shi, muzaffar na ganin haka ya zare takobinsa ya daka musu tsawa ya ce “yaku jama’ar lamfur nayi rantsuwa da taurari ababen bautawa agareni duk wanda ya gabato gareni daga cikinku da muguwar nufaka sai na aikashi duniyar nan da in an tafi ba’adawo wa, na maishe da yaransa marayu, matansa su kasance zawara, inda mai inkari akan maganata sai ya kusanto ni yaga”

Jama’ar birnin lamfur suka fusata da jin kalaman muzaffar, suka afkamasa da yaki, muzaffar ya fada cikinsu da yaki yana mai sara da sukansu, su ko suka wanzu suna kara kusantar muzaffar yayin dayake sada su da ajalinsu, yayin da suka farga ga irin barnar da muzaffar keyi musu suka kaga ya raunata musu mutane ba’adadi duk da bai kashe kowa, ai sai suka ja baya.

a sannan ne muzaffar ya hango kura ta turnuke gabashin birnin, nan fa ya tsayu yana duban wannan guguwa koda guguwar ta gabato garesu sai yaga gagarumar rundunace ta mayaka cikin shigan yaki sun durfafosu,

wannan runduna dai ba rundunar kowa bace face ta sarki Huntaru bin Jaujas tare da dakarunsa, Tuni labari ya kaiwa sarki huntaru cewa wani badakare ya shigo kasarsa ya hanu ga cin abincin da mutanensa suka bashi wanda musabbabin hakan ya sanya jama’ar birnin suka far masa inda ya ruga Raunata masa mutane. hakan ya sanya sarki huntaru yin hawa da kanshi don kawar da muzaffar daga ban kasa.

koda karisowar dakarun nan sai suka tsaya a nesa da muzaffar sarki huntaru ya karewa muzaffar kallo cikin bacin rai da fusata ya nufo gareshi, ai koda muzaffar yaga haka sai yai maza ya gyara rikon takobinsa yana tsumayen isowar sarki huntaru…

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*