FARATAN ZAKI littafi na daya 1 part A

FARATAN ZAKI
Littafi na daya 1
na Shuraihu Usman
Part A
© Shuraih 99% – 2020
.
Saurayine kyakkyawa tafe bisa kan ingarman doki, yana shara masifaffen gudu tamkar zai kure duniya, wannan saurayin ya wanzu yana keta dazuzzuka, kwazazzabai gami da koramu.

matashin saurayin mai suna Muzaffar yaci alwashin koda zai gamu da ajalinsa bisa ga batun mutane akan wurin daya nufa sai ya isa wannan wuri ya isar da bukatansa, shi dai muzaffar ya fito ne daga wata alkarya mai suna DUMBAZUR SAHIR, cikin birnin MARHABUR SIHIR,

birnin marhabur sihir birni ne da aka sana’anta shi da alkaluman tsafi hadi da sihiri, Birnin na karkashin wani azzalumin sarki ne mai suna basdur, duk da mutanen birnin marhabur sihir suna rayuwa cikin kunci gamida takurar rayuwa da suke fuskanta daga sarki Basdur, hakan bai sanya sun canja birni ba, domin kuwa gaba dayan biranen dake Alkaryan dumbazur sahir suma suna fuskantar kwatankwacin wannan ukuba da mutanen birnin marhabur sihir ke fuskanta.

Muzaffar ya cigaba da keta dazuzzuka yana tsala masifaffen gudu bisa kan dokinsa, babu abunda ke tsaida shi dare ko rana, komai duhuwar dare baya tsagaitawa da tafiya, burin muzaffar guda daya ne a duniya shine ya isa KOGON SARKIN ZAKUNA ya ciro FARATAN SARKIN ZAKUNA dun yiwa babban abokinsa kuma amininsa maganin cutar data kama shi.

lallai muzaffar yaci alwashi gamida alkawari bazai koma birnin Marhabur sihir ba batare da FARATAN ZAKI ba koda kuwa zai riski ajalinsa.

wata rana cikin ranaku muzaffar na tsala azababben gudu cikin daji kamar kullum, kwatsam babu zato babu tsammani sai dokin nasa yaja ya turje yaki gaba yaki baya, muzaffar ya zaburi dokin don yayi gaba amma dokin ya ki, maimakon ma dokin yayi gaba sai ya fara rimi yana kokarin kayar da muzaffar dake bayansa, cikin sauri muzaffar ya daka tsalle ya dirgo kasa, sannan ya fara karema hanyar kallo, ko shakka baya yi wani abun cutarwa dokin nasa ya hango masa, cikin yadda dakai ya zare takobinsa ya nufi hanyar.

ai yana kara gaba kunnuwansa suka fara dauko masa wani irin sauti mara dadin sauraro sautin yafi kama da a kirashi da sautin gurnanin wata mugunyar dabba, ai babu zato babu tsammani wani jibgegen mutum ya dirgo daga saman wata jibgegiyar bishiya dake kusa da muzaffar da niyyar ya dirgo a saman kan muzaffar, hucin zuwan mutumin ne ya sanya muzaffar saurin kallon saman kansa inda yai arba da katon yana kusantoshi, cikin azama ya kauce katon ya fado bisa kan kasa, muzaffar ya juyo ya dubi katon takobinsa a zare, katon da babu komai a hannunsa ya cigaba da gurnani yana kallon muzaffar yana dalalar da yawu daga bakinsa.

bayan dakiku biyu sai katon nan yayi kukan kura ya fada kan muzaffar, yana karisowa muzaffar ya sanya takobinsa ya tsargeshi gida biyu, nan katon ya fadi kasa matacce.

Muzaffar ya maida takobinsa cikin kufenta ya nufi dokinsa, yana niyyar hawa dokin kenan kunnuwansa suka sake dauko masa irin sautin gurnanin nan na baya, sannan lokaci guda irin kattin nan suka rika dirdirgowa daga saman bishiyun dake dajin, kafin wani lokaci har sun mamaye muzaffar, sudai wayannan karti adadinsu yakai dubu uku suna rike da yan kananun wukake masu kaifi, kartin suka fara dukan kirazansu suna wani irin gurnani tamkar zakuna, can suka dare sai ga wani jibgegen kato ya daro tsakiyarsu shidai wannan kato duk ya fisu girma da murmurde wan jiki, katon na rike da jibgegiyar guduma na bakin karfe a hannunsa.

koda karasowar katon sai ya dubi muzaffar cikin bacin rai yace “yakai wannan mutumin kai sani ka aikata mafi munin aika aika, ga dan uwanmu wanda hakan ya janyo maka hukuncin mummunan kisa daga gareni, ni Shu’ubaru dan jimganu nayi rantsuwa da jini abun sha, ga ni da mutanena da kuma naman bil’adama daya kasance abinci garemu, sai na sada ka da ajalinka sannan na zuke jinin jikinka da ranka na shanye daga karshe na riga yankan naman jikinka inaci, amma kafin nan bari na fara da wannan”

shu’ubaru ya damko gawar katon nan da Muzaffar ya tsargeshi gida biyu, ya wangame bakinsa yafara gatsar naman dan uwan nasu.

koda muzaffar yaga haka sai ya daka wa shu’abaru tsawa ya ce “yaku wayannan katti kuyi sani cewa ni matafiyi ne ban zo gareku da mummunan nufaka ba, asalima dan uwanku shi yai nufin kasheni ni kuma na kare kaina, dun haka ina mai baku shawara da tun wuri ku yi tafiyarku, muddin ko kukace zaku yakeni ina mai rantsuwa da taurari duk sai na sada ku da ajalinku.”

Shu’abaru najin kalaman muzaffar sai yaji tamkar muzaffar ya watsa mai ruwan zafi ne nan da nan yai wa mutanensa umarni da su shigewa muzaffar, nan fa wasu mutum biyu suka falfala da masifaffen gudu sukai kan muzaffar, ai suna isowa suka daka tsalle dukkansu suka kaiwa muzaffar munanan hari da nufin suyi masa kisan kwaf daya.

cikin salon bajinta da sanin tuggun gumurzu muzaffar ya wurkita jikinsa ya kauce wa harin kattin kuma lokaci guda cikin azama ya juyo ya fille musu kawuna da takobinsa, wannan abu yayi matukar kara harzuka shu’ubaru nan yaiwa mutanensa tsawa dukkansu sukai kan Muzaffar.

muzaffar ya gyara tsayuwa yana jiran isowarsu ai koda karisowarsu sai ya shigesu da sara da suka, nan fa ya wanzu yana mai sada su da ajalinsu, ya tsayu a tsakiyarsu tamkar iblishi, tamkar manomi na girbe a gona, suko suka yanyameshi tamkar farin annoba, nan fa kunnuwa suka kurumta da jin sautin komai face na karar takobi, da wukaken kartin nan, sassan jikkunan kartin suka ringa yawatawa a sararin samaniya, kasa ta fara rinewa da jini.

koda shu’ubaru yaga muzaffar sai ragargazar mutanensa yake sai ya fusata ainun ya kwarara uban ihu, daya karade dajin baki daya ya kuma haddasa tsayuwar yakin, shu’ubaru ya daka wa mutanensa tsawa yace “ku gafara can malalatan banza ace mutum guda ya gagareku, “.

Shu’ubaru ya jinjina gudumar dake hannunsa sannan yai kururuwa yai kan muzaffar, ganin haka shima muzaffar yayi kukan kura ya dunfari shu’ubaru da takobinsa tsirara

sai da ya rage baifi zira’i uku tsakaninsu ba ai sai Muzaffar ya daka uban tsalle a saman yai juyi ya kawo ma shu’ubaru mummunan sara a wuya da nufin ya raba zumuncin dake tsakanin kanshi da gangar jikinsa, cikin sauri shu’ubaru ya kare saran da gudumar hannunsa, sabida karfin saran sai da shu’ubaru yayi baya.

muzaffar bai tsagaita ba ya cigaba da kaiwa shu’ubaru mugayen sara da takobinsa shu’ubaru na karewa shima yana kawo masa munanan duka da gudunar dake hannunsa muzaffar na gocewa, nan fa suka wanzu suna kaiwa junansu munanan hare hare cikin bakin nufaka da nufin yiwa junansu kisan gilla, shidai shu’ubaru kokari ya ke ya dagargaza kan Muzaffar da Gudumarsa, shiko muzaffar kokari yake ya soke shu’ubaru da takobinsa a ciki.

Ragowar baradan shu’ubaru suka tsayu suna kallon masifaffen gumurzun dake wakana tsakanin shugabansu da muzaffar cikin tsoro da rudu, gani suke a kowanne lokaci muzaffar zai iya samun lagon shugaban nasu,
koda shu’ubaru yaga wankin hula na neman ya kaishi dare sai yai kukan kura ya yadda gudumarsa ya dubi muzaffar yai masa inkiya daya shigo, muzaffar ya zaburo ya kawo mai sara caraf shu’ubaru ya rike masa hannu, kafin muzaffar yai wani yunkuri tuni har ya gabza mai naushi a ruwan ciki, muzaffar yayi baya kamar zai fadi, shu’ubaru ya sake yibmasa inkiya daya shigo, nan fa muzaffar ya fusata yai karaji ya falfala da masifaffen gudu zuwa kan shu’ubaru koda ya kusan karisowa gabansa sai ya daka tsalle yai sama ya sanya kafarsa da nufin ya doki shu’ubaru aka nanma shu’ubaru yai caraf ya rike kafar tasa yai wulli da shi, muzaffar ya fusata matukar fusata ya mike yana nishi bakinsa na fitar da hayaki ya kifu akan shu’ubaru suka kacame da sabon azabben gumurzu suka wanzu suna kaiwa junansu naushi da bugu hadi da mangari, a wannan gumurzu sai da shu’ubaru yai wa muzaffar kaca kaca, kasancewar ya fishi karfin damtse kuma naushinsa na da matukar nauyi sabanin na muzaffar, tun muzaffar na iya kai duka har ya zamanto baya iyayi, kare kansa ma dakyar yake yi.

shu’ubaru ya shammaci muzaffar ya sureshi da nufin ya kifa da wani jibgegen dutse dake kusa da su, sai da ya daga muzaffar sama ai sai muzaffar ya wurkita jikinsa a saman ya ya sanya dukkan karfinsa ya damki kan shu’ubaru ya hada da dutsin, kan ya dagargaje a jikin dutsin, shu’ubaru ya kife matacce, ragowar baradansa da suka ga abunda ya afku ga shugabansu kuma dama tuni sun tsorata da al’amarin muzaffar sai suka tsorata suka fada daji a guje.

muzaffar ya mike ya shafa magani a raunin daya ji sannan ya kama dokinsa ya hawa ya zabureshi ya cigaba da tafiya….

Na kusan kammala littafin nan kuma ina nufin in bugashi ne ya shiga kasuwa… Abokai ko menene Shawarar ku akan hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*